Kasar Saliyo Na Neman Afuwa Wajen FIFA — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Kasar Saliyo Na Neman Afuwa Wajen FIFA

Published

on


Kasar Saliyo ta aike da wasika zuwa ga hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, inda take neman hukumar ta janye matakin da ta dauka, na dakatar da ita daga shiga wasanni.

FIFA ta haramtawa kasar Saliyo shiga wasanni a makon da ya gabata, saboda katsalandan din da gwamnatin kasar ta yi a cikin harkokin hukumar kula da wasan kwallon kafar kasar.

Rikicin cikin gidan ya samo asali ne, bayanda hukumar yakar cin hanci da rashawa ta kasar, ta yi yunkurin sauke Isha Johansen da Christopher Kamara, wato shugabar hukumar kwallon kasar ta Saliyo da kuma sakataren hukumar daga mukamansu, bisa zargin sun aikata laifukan cin hanci da rashawa.

Bayan kamala taron gaggawa a ranar Litinin, tsakanin jami’an hukumar kwallon kafar ta Saliyo da gwamnatin kasar, jami’an kwallon kafar kasar suka aike da wasikar neman FIFA ta dage haramcin wasannin da ta kakaba musu, domin basu damar buga wasa tsakaninsu da Ghana, na neman cancantar halartar gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Sai dai har yanzu hukumar kwallon kafa ta Duniya batace komai akan lamarin ba amma ana ganin nan da ranar Juma’a hukumar za ta bayyana matsayinta akan bukatar ta kasar Saliyo.

Advertisement
Click to comment

labarai