Kashi 39% Kacal Na ‘Yan Nijeriya Ke Amfani Da Bandakin Zamani –UNICEF — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIWON LAFIYA

Kashi 39% Kacal Na ‘Yan Nijeriya Ke Amfani Da Bandakin Zamani –UNICEF

Published

on


Asusun kulawa da gidauniyar gaggawa na kananan yara na majalisar dinkin duniya ya bayyanacewar kashi 39 na ‘yan Nijeriya suke amfani da masai na zamani, wadanda kawaib kawai iyalann gida daya ne suke amfani da shi.

Wannan al’amarin duk yana faruwa ne duk kuwa da yake ana yaki da al’adarnan ta yin kashi a fili, inda kuma kasar Nijeriya ce take da mutane milyan 47, wadanda suke zaune a kauyuka, da kuma muatne milyan 11.6 wadanda suke da zama a birane abin ya fara samun wata karbuwa.

Ms Martha Hokonya wadda babban jami’ace ta banagaren samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma kulawa da tsaftace muhalli na asusun taimakon gaggawa akan al’amurann da suka shafi yara na majalisar dinkin duniya, ita ce wadda ta bayyana hakan lokacin taron kwana biyu na ganawa da ‘yan jarida a Fatakwal babban birnin jihar.

Ta bayyana cewar ita kididdigar an same tane ta hadin kan wata kungiya mai suna Miltiple Cluster Serby na shekarar 2017 da aka yi musamman saboda kasar Nijeriya, musamman ma akan sanya jari akan al’amarin da ya shafi tsaftace muhalli, abinda ta ce abu ne mai riba ga kowa.

Da take nuna jin dadinta akan kokarinda gwamnatin jihar Ribers ta yi, saboda bin ka’idar data yi, akan kason kudin hadin gwiwa na aiki, abinda tace ya taimaka matuka gaya, wajen inganta tsaftace muhalli, da kuma rage yin kashi (ba haya) a fili, wanda abin ya zama wani al’amari a jihar. Duk da hakan Hokonya ta kara jaddada cewar hjar yanzu da akwai bukata ta, a kara gingina wuraren ba haya wao masai da kuma tunawa da muhimmancin shi wajen rage yaduwar cuta.

Ta bayyana cewarsaboda a samu cimma muradan SDG wanda WASH tana zaman kanta ne, da akwai bukatar su ma al’umma, su kasance a cikin al’amarin, wato ayyukan da nahiyar Turai da kuma sauran wasu abokan tafiya suke taimakawa.

Bugu da kari ta ce wasu daga cikin al’amuran da suka kamata aci giba da aiwatar da su, bai kuma kamata abar wani a baya ba, al’amarin ya kamata ace kowa yana ciki, a kuma mayar da hankali akan yin adalci, rage nuna bambanci, ba kuma nuna bambanci tsakanin maza da kuma mata, saboda  kowa yana da nashi muhimmancin. Ga kuma taimakawa mata, kuma bullo da wani shiri na taimaka ma mata.

Hakanan ma al’amarin daya shafi ruwa na kauyuka, manajan shiri na al’ummar Kpokpo da suka hada da karamar hukumar Opobo/ Nkoro Fineboy Fineboy ya ce tun dai bayyanar ayyukan shekarar 2017, ba wani labarin da aka samu na barkewar annobar ciwon da ake samu ruwa da kuma rashin tsafta.

Ta kara bayyana cewar shi tsarin wanda ana amfani ne da solar wajen samar da wuta ya kawo ma al’ummar wurin, wajen gane amfanin tasafatace muhalli, da kuma amfanin tsaftataccen ruwan sha, musamman ma ga rayuwar yara.

Advertisement
Click to comment

labarai