Kotun Kasar Masar Ta Yanke Ma Mutum 17 Hukuncin Kisa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotun Kasar Masar Ta Yanke Ma Mutum 17 Hukuncin Kisa

Published

on


Babbar kotun sojin kasar Masar, ta yanke wa mutum 17, da aka same su da laifin kai harin ta’addanci kan Mujami’un Kibdawa Kiristoci a tsakanin shekarar 2016 da 2017, wanda ya yi sanadiyar rayukan mutane da dama.

Sannan Kotun ta yanke wa wasu mutum 19 da suma aka same su da hannun cikin harin ta’addanci hukuncin daurin rai da rai, wanda yake daidai da shekaru 25 a gidan kasu, a dokar kasar Masar din, sai kuma karin wasu mutum 10 da suke da hannu wajen kai harin, su kuma an yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 zuwa 15.

Duk da wadanda ake zargin zasu iya daukaka kara a kan hukuncin, wata shara’a ta daban kuma an zargi su wadannan mutanen da zamuwa ‘yan kungiyar ta’addanci ta ISIS.

A watan Afrilun shekarar 2017 ne, wasu ‘yan kunar bakin wake suka tada bama-bamai a mujami’ar Kibdawa dake garin Alexandria da kuma gabar bahar maliya, inda suka jawo sanadiyyar mutuwar mutane 46 lokacin gudanar da wani bikin ‘yan addinin Kiristanci.

A shekarar 2016 ma, an kai irin wannan harin a wata mujami’ar Kibdawan dake garin Alkahira, wacce ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 28.

Advertisement
Click to comment

labarai