Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Saudiyya Ta Dakata Da Hare-Hare Akan Al'ummar Yemen — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Saudiyya Ta Dakata Da Hare-Hare Akan Al’ummar Yemen

Published

on


Kungiyar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya ta bukaci kasar Saudiyya da ta tsagaita hare-haren da ta ke kaiwa al’ummar kasar Yemen, hare-haren sun fi shafar fararen hula.

Kungiyar kare hakkin kananan yara ta majalisar ma ta yi irin wannan kiran, ganin yadda kasar Saudiyyan take kai hare-haren ta akan kananan yara, a kwanakin baya yara 40 ne suka rasa ransu a wani harin da Saudiyyan ta kai ta sama.

Wannan batun ya kara tasowa ne bayan da kasar Saudiyya ta sake shiga wani rikicin na bacewar dan jarida mai adawa da manufofin gwamnatin Saudiyya, Jamal Khashoggi ya shahara da sukan gwamnatin Saudiyyan, musamman kan batun yakin da take yi a kasar Yemen.

An kiyasta adadin yaran da harin Saudiyyan ya kashe, ya kai akalla 1,248, sannan wani adadin da ya fi haka kuma sun samu raunuka daban-daban, sannan ga yunwa da take addabar miliyoyin yara a kasar ta Yemen.

Kungiyoyin kare hakkin Bil’adama suna zargin kasar ta Saudiyya da kai hare-hare kan fararen hula, inda mata da kananan yara suka fi mutuwa a hare-haren na kasar Saudiyya.

Advertisement
Click to comment

labarai