Makomar Rubutun Hannu A Zamanin Kimiyya Da Fasaha — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIMIYYA

Makomar Rubutun Hannu A Zamanin Kimiyya Da Fasaha

Published

on


Babu shakka rubutun hannu ya ragu sosai, a inda rubutu da madannai na kwamfuta (Keyboard) da wanda ake yi akan gilishi (Screen) yake neman maye gurbin rubutun hannu akan takarda, hatta sa hannu akwai abubuwan da zasu maye gurbin sa.

Yaran da suka zo a wannan zamanin basu san dadin rubutun hannu ba, sai dais u shafa gilishin waya, ko su latsa madannan kwamfuta kawai, a wasu kasashen ma sam basa yin rubutun hannu, abun tambaya me za a yi hasara in aka daina rubutun hannu?

Da duk dalibi dole sai yayi rubutun hannu a takarda in yaje makaranta, amma yanzu abun ba haka yake ba, kasashen kamar kasar Finland tuni suka watsi da koyar da rubutun hannu, inda suka maye gurbinsa da koyar da rubutun da madannai, a amurka kuwa tun a shekarar 2013 aka daina ba rubutun hannu muhimmanci a tsarin karatu, duk akwai jihohi ‘yan kalilan kamar jihar Arizona su har yau suna baiwa rubutun hannu muhimmanci.

Akwai masanan da suke ganin koyar da rubutun hannu yana da nashi amfanin, Anne Trubek ta ce koyan rubutun hannu yana sanya wani nau’in kwarewa a fagen ilimi, wato yana sanya mutum ya dinga cika duk aikin da zai yi, ta kwatanta rubutun hannu da tukin mota.

Ta ce rubutu da madannai yana rage tunani sosai, sabanin in mutum yana rubutu da hannu, zai yi kuskure kuma ya gano kuskuren da kanshi sanna ya gyara kuskuren, in da madannani yake ba fa lallai ya iya gane kuskuren ba da kanshi balle ma ya gyara, sannan kamar dai tukin mota in muna tafiya muna ganin abubuwa a gefen titi toh haka rubutu ma, yana kara bude mana kwakwalwa wajen tunani.

Trubek ta ce tayi mamaki yadda aka fara watsar da rubutun hannu, duk ta ce ta yarda dalibai sun fi koyon karatu da sauri in suna mafani da madannai sabanin rubutun hannu, misali dalibai suna iya koyon rubuta kalmomi ba tare da sun kalli madannai ba, sannan suna koyon saurin rubutu da madannan.

Misali a kasar Finland, wacce take daya daga cikin kasashen turai da suke kan gaba wajen tsarin koyarwa na zamani, a shekarar 2014 aka yi wa tsarin ilimin kasar kwaskwarima, inda aka zabi a fi baiwa rubutu da madannai muhimmanci sama da rubutun hannu, aka maye gurbin littafin rubutu da kwamfuta.

Ita kuma Harmanen ta ce dalilin da yasa rubutun hannu ya ragu shine an samu fasahohi na zamani da suka maye gurbin rubutun hannu, sannan kuma mafi yawan mutane suna amfani da madannai na kwamfuta a rayuwarsu ta aiki bayan sun kammala karatu, kusan duk ayyukan da zasu yi ba da rubutun hannu zasu yi ba, da kwamfuta ne, don haka dole da madannai zasu yi rubutu.

Masana da dama suna ganin rubutun hannu yana taimakon kwakwalwar dana dam sosai, akwai bincike da masana suka yi wanda yake tabbatar da wannan, misali an tabbatar da cewa rubutun hannu yana sa motsin hannu da yake nuna kwarewa wajen amfani da yatsun wajen yin aiki, wani masani kuma yana ganin rubutun hannu, da rubutu da madannai suna amfani daban-daban.

Wani masani yace, ‘akwai amfani sosai a karatu da rubutu, kafin mutum ya yi rubutu mai kyau wanda za’a gane toh lallai yana bukatar kwarewar motsin ‘yan yatsu, sannan dole mutum ya zama ya sanya hankali da lura sosai wajen yin karatu ko rubutun hannu, kuma abu ne da dole sai mutum ya koyi yadda ake yi, a wajen rubutu da karatu kwakwalwa tana wasu ayyuka da bata yi in ana amfani da madannai na kwamfuta ko wayar hannu.’

A wani bincike na daban kuwa an iya tabbatar da cewa kwakwalwa tafi rike abunda aka karanta aka rubuta da hannu, sannan rubutun hannu yana matukar taimakon kananan yara wajen koyon karatu, misali anyi wani gwaji da wasu yara kanana inda aka sa wasu suka rubuta haruffa da hannu, wasu kuma da madannai na kwamfuta, lokaci da akayi musu gwaji da inji mai gani har hanji an gano cewa kwakwalwar yaran da suka yi rubutu da hannu tafi saurin gane haruffa in ta gan su sabanin kwakwalwar wadanda suka rubuta da madannan kwamfuta.

Don haka masana da dama suke ganin lallai rubutun hannu yana sa karin budewar kwakwalwa, iya zane-zane, sannan yana matukar taimakon dalibai su gane karatu cikin sauki.

Duk da haka akwai fasahohi da ake ganin zasu maye gurbin takarda da alkalami, kai har ma da fasahar da zaka furta kalma sai ta rubuta maka kalmar, misali akwai Siri na kamfanin Apple, da Cortana na Kamfanin Microsoft, shekaru kadan da suka wuce marubuta dole da takarda da alkalami zasu yi rubutu, amma yau batun ba haka bane.

Da gaske rubutun hannu yana matukar raguwa, zamani yazo da fasahohi masu yawan gaske, amma fa ba wanda zai manta muhimmancin rubutun hannu, fasahohin da suka fito kamar wayar hannu, madannan kwamfuta, da i-mel, sun kasa bishi darajar alkalami, rubutun hannu kuwa har yau abu ne mai daraja sosai.

Ko da zamani yazo an daina rubutun hannu to ba za a daina girmama littafai da aka rubuta su da hannu ba, ba za a daina girmama rubutun hannu ba gaba dayanshi, saboda abu ne mai matukar daraja da muhimmanci.

Advertisement
Click to comment

labarai