Masana Sun Yi Gargadi Kan Amfani Da Sinadaran Sauya Launin fata — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIWON LAFIYA

Masana Sun Yi Gargadi Kan Amfani Da Sinadaran Sauya Launin fata

Published

on


Masana ilimin fatar dan adam da lafiyar al’umma sun ba ‘yan Nijeriya shawara akan babbar matsalar da za a iya shiga a sanadiyyar yin amfani da sinadarai ko abubuwan da ke launa fatar dan adam.

Wannan kuwa launin walau sauya fata daga yadda aka santa ko wani abu mai kama da hakan. Abin da kuma daga karshe yana iya kai masu aikatawa ga shiga wata babbar matsala. Kadan daga cikin Cututtukan da za a kamuwa da su suna da nasaba da fata, sai kuma cutar koda kansa da dai sauran su.

Da take jawabi a wani taro na tsarin wayar da kan al’umma wanda aka yi a Lagos cikin makon daya gabata, shugaban wata kungiya ko kuma gidauniya mai suna Black is Beauty (bakar fata abar ayi alfahari da ita ne) Dakta Chidinma Gab- Okafor, ya bayyana hadarin da aka iya shiga saboda kokarin canza kalar fatar jiki, sabodac kokarin da ake yi na  gyara ainihin halittar da aka san mutum da ita, wannan kuma shi ke sanadiyar mutuwa ta wadanda suke da wannan sha’awa ta canza fatar jikinsu.

Gab – Okafor ta bayyana cewar da akwai bukatar a rika sa ido akan yadda aka fitar da su kayayyakin da ake canza fatar jiki dasu, saboda fata tab rika haske, abin yana karuwa a Nijeriya, wannan kuma abin ba a iya danganta shi da, shekara, jinsin mace ko kuma na namiji, aure ko kuma wane irin halin tattalin arziki mutum yake.

Ta kara bayyana cewar masu yin su kayayyakin da kuma masu shigo dasu basu wani la’akari da wasu dokoki, ko kuma nagarta su kayayyakin, wanda ta haka ne ake shigo da wadanda basu da nagarta, zsa kuma su iya cutar da jiki, sune aka samu a kasuwannin mu kullun.

Ta kara jaddada cewar su sinadarorin da aka hada ana yin kayayyakin da ake kokarin canza fatar jiki, suna iya samarc da wasu matsalolin da suka shafi lafiya,a jiki kamar cututtukan fata matsalar yadda jini ke tafiya zuwa wuraren da ya dace da dai sauransu.

Kamar dai yadda ta kara yin bayani “Zai yi wuya a rasa mace ‘yar Nijeriya wadda take amfani man shafawa kamar samfuri goma sha biyu, wadanda kuma baa bin mamaki bane idan aka ce sun kunshi wadansu sinadarai wadanda zasu iya cutarwa 158,ya yin da su kuma maza suna amfani da mai samfuri shida, wadanda su kuma sun kunshi wasu sinadarai 85 a kullun rana

“ Manaya suna amfani da wasu sinadarai 17 yayin da su kuma yara suna amafani da guda shida,a kullun rana. Dukkan wadannan nau’oin man na shafa suna shiga cikin jikinmu saboda gaba su samar da wata matsala ga shi jikin”.

Donhaka shi yasa ta yi kira da a dauki wasu tsauraran matakai da wasu tsare tsare, wanda gwamnati ya kamata ta sa doka, saboda a rika sa ido yadda ake shigowa da su kayayyakin, musamman ma shigo da su kayayyakin da zasu iya cutarwa, wadanda tuni suna samar da matsala ga ‘yan Nijeriya musamman mata, kamar yadda ake yi a United Kingdom da kuma Amurka.

Tun farko dai Rabaran Monsignor John Aniagwu ya yi kira ga matasan Nijeriya su maida hankalinsu, wajen koyon sana’oi daban daban, maimakon su sa kansu ko kuma mayar da hankalinsu wajen yin abubuan da ba zasu taimaka masu da komai ba.

Shi ma da yake jawabi a wajen bayar da tashi gudnmawar wani kwararre a bangaren kiwon lafiya, ya kara jawo hankalin mutane akan, cewar abin da mutum yake shafawa a ajikin shi, yana iya shiga ta cikin musamman kofofin gashin jiki, musamman ma idan suka shiga koda suna iya kawo babbar matsala da suke kira da ‘reanal failure’.

Ta bayyana cewa, fata jiki wata aba ce da take da rai, ana iya inganta ta, ta hanyar cin abincin da ya kamata, ba kuma dole ba ne sai an damu da ko mene ne aka sa ba.

Wadanda suka halarci shi taron na ayar da kan al’ukmma an horar da su yadda zau yi amfani da wani abin da watakila zasu ciro shi a gona, saboda su yi abin da bai da wata nasaba da kayayyakin shafe shafen zamani wadanda suke lalata jiki.

Advertisement
Click to comment

labarai