Real Madrid Ba Ta Matsalar Ronaldo -Ramos — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ba Ta Matsalar Ronaldo -Ramos

Published

on


Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos, ya bayyana cewa kungiyar bata matsalar Ronaldo duk da cewa basa samun damar zura kwallaye a raga da yawa a wannan kakar.

Ramos ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labarai a shirye shiryen da yakeyi na bugawa kasar Sipaniya wasa a karshen satinnan inda yace nan gaba kadan zasu dawo yadda suke kamar da.

Real Madrid dai ta buga wasanni hudu ba tare data zura kwallo a raga ba ciki kuma tayi rashin nasara a wasanni biyu a laliga da kuma gasar zakarun turai wanda hakan yasa aka fara tunanin rashin Ronaldo ne.

“Lokacin da yake tare damu ma wani lokacin muna shan wahala wajen rashin zura kwallo a raga saboda haka ba sabon abu bane a kungiyar mu kuma zamu farfado kamar yadda aka sammu a baya” in ji Ramos

Ya ci gaba da cewa ‘Ronaldo babban dan wasa ne wanda yake iya zura kwallo a raga a kowanne yanayi amma kuma halin da muka samu kanmu aciki ba matsalarsa bane yanayi ne kawai na wasa”

Ronaldo dai yakoma Juventus daga Real Madrid akan kudi kusan fam miliyan 105 wanda hakan yakawo karshen zamansa na shekara 9 a kungiyar inda ya lashe kofuna da dama sannan ya zura kwallaye sama da 500.

Advertisement
Click to comment

labarai