’Yan Sanda Na Farautar Ma’aikaciyar Da Ta Kashe Uwargidanta A Abuja — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Na Farautar Ma’aikaciyar Da Ta Kashe Uwargidanta A Abuja

Published

on


Rundunar ‘yan sanda suna farautar wata mata mai suna Beckly Johnson bisa zargin kisar Yemisi Haasz a gidanta dake Asokoro cikin garin Abuja, tare da yin awan gaba da kayayyakinta. Kakakin rundunar ‘yan sandar babban birnin tarayya Anjuguri Manzah ya ce “rundunar ‘yan sanda tana gudanar da aiki a kan lamarin, ya kara da cewa suna kokarin yadda za a samu nasarar cafke wanda ake zargi. An dai yi jana’izar Haasz ranar Laraba a Apo cikin garin Abuja.

Wata kawar marigayiyar mai suna Ruby Galore ta ce, lamarin ya faru ne ranar 23 ga watan Satumbar shekarar 2018. Ta kuma bayyana cewa, Haasz tana cikin gida ita daya tare da karamar yarinyarta sai Johnson ta shiga gidan. Ta ci gaba da cewa, Johnson ta cika mata wuka sannan kuma ta saka karamar bindiga ta harbe ta.

A cewar ta, bayan ta kashe ta sannan kuma ta kulle ta a daki tare da yarinyarta, ta kuma yi awan gaba da gwalagwalai, kudade, wayan tarho da kuma wadansu sauran kayayyaki. Ta ce “kawarta ta auri wani dan kasar Isreala kuma baya yawan zama. Tana zaune ne a cikin gidan tare da yarinyarta, ‘yar aiki da kuma Becky Johnson.

“A ranar da lamarin ya faru, Becky ta kashe ta sannan ta kulle ta a cikin daki tare da yarinyarta, inda ta yi awan gaba da dukiyoyi masu yawa.”

Galore ta bayyana cewa, da farko dai masu gadin gidan sun hana ta fita da kayayyakin amma sai da ta jira har zuwa karfe 11 na dare kafin ta samu ta fita da kayayyakin.

“Lokacin da ta gaya wa masu gadin za ta yi tafi zuwa kauye, shi ya sa take kokarin tattara kayanta, sun dai hana ta fida inda suka ce Yemisi Haasz ba ta gaya musu za ta yi tafi ya ba.

“Sun kira ta amma ba a daga ba. Becky ta gaya wa masu gadin cewa za ta je ta kira mai mota, daga nan sai ta kira maigidan inda daga nan ne ta gudu har yau ba a ganta ba,” inji shi.

Galore ta kuma bayyana cewa, an sami gawar Haasz cikin jini a dakinta, bayan mijinta wanda yake kasar waje ya bawa masu gadi izinin balle kofar. Ta kuma nuna takaicinta a kan yadda ake gudanar bincike kisan, sannan kuma tana tamuwa a kan yadda Johnson ‘yar a salin jihar Akwa Ibom ta gudu daga fuskantar shari’a.

Advertisement
Click to comment

labarai