‘Yan Sanda Sun Ceto Shugaban Karamar Hukuma Da Dansa Daga Hannun Masu Garkuwa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda Sun Ceto Shugaban Karamar Hukuma Da Dansa Daga Hannun Masu Garkuwa

Published

on


Rundunar ‘yan sandar jihar Imo ta samu nasarar ceto shugaban karamar hukumar Ihiala dake jihar Anambra mai suna Ifeanyi Odimegwu. Sannan kuma an samu nasarar ceto dansa mai suna Tochi Odimegwu da kuma direbansa Boniface Uche wadanda suka yi garkuwa da su. Kwamishinan ‘yan sandar jihar Imo Dasuki Galadanchi shi ya bayyana hakan a garin Owerri, ya ce, an sace shugaban karamar hukumar ne a kan babban hanyar Owerri-Port Harcourt ranar Lahadi da safe. Galadanchi ya kara da cewa, lamarin ya faru ne a Umuapu lokacin da shugaban karamar hukumar da dansa da kuma direbansa suke dawo wa daga garin Owerri bayan sun gama halattan wani abiki a Cocin jihar Ribas. Ya ci gaba da cewa “an dai yi garkuwa da shugaban ne lokacin da yake dawo wa daga Elele dake jihar Ribas bayan ya halacci zaman Coci. An yi garkuwa da shi tare da direbansa mai suna Boniface Uche da kuma dansa mai suna Tochi a Umuapu. Lokacin da aka ji karar bindiga, sai jami’an ‘yan sandar dake bakin aiki suka yi gaggawar zuwa wajen.

“Yayin da suka isa wajen, jami’an ‘yan sandar sun bule wuta a kan masu garkuwan inda suka samu nasarar ceto shugaban tare da dansa da kuma direbansa. Jami’an ‘yan sandar wanda lamarin ya faru a gaban idanunsu tare da taimakon ‘yan bangar Ihie da kuma mutanan garin Obrugo sun shiga cikin dajin Umuapu domin neman su.”

Kwamishinan ya tabbatar da cewa, lokacin da masu garkuwan suka ga jami’an ‘yan sanda a cikin dajin, sai suka gudu tare kudade masu yawa da wayar tarho sannan kuma da sauran kayayyaki masu daraja. Ya kuma kara da cewa, shugaban karamar hukumar ya yi matukar kaduwa inda aka zargaya da shi asibiti. Galadanchi ya kuma bayyana cewa, rundunar ‘yan sanda suna binciken duk wani bayani wanda suka samu daga wajen wadanda aka yi garkuwa da su.

Advertisement
Click to comment

labarai