’Yar Nijeriya Ta Kashe Kanta Bayan An Kulle Mata Shago A Ghana — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

’Yar Nijeriya Ta Kashe Kanta Bayan An Kulle Mata Shago A Ghana

Published

on


Saboda an rufe mata shago wanda hukumomin kasar Ghana suka bada umarnin yin hakan, wata mata ‘yar asalin Nijeriya wadda kuma take da ‘ya’ya uku ta kashe kanta, kamar dai yadda kungiyar ‘yan kasuwar Nijeriya mazauna kasar (NANTs) Ghana suka bayyana haka ranar Talata.

‘Yan kungiyar sun bayyana haka ne lokacin da Jaridar Leadership ta kai ma mataimakin shugaban kasa na musamman akan harkokin kasashen waje da kuma al’ummar Nijeriya wadanda suke kasashen waje, Abike Dabiri- Erewa saboda a samu sab akin Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan shi al’amarin.

Shugaban kungiyar NANTS ta Ghana Chukwuemeka Nnaji ya bayyana cewar Stella Ogonna Okpaleke ‘yan Nijeriya ce wadda aka rufe shgunanta, saboda ta kasa cimma ka’idojin kasuwanci,  Mwadanda kasar Ghana suka sa sai ta kashe kanta ranar 22 ga watan Satumba 22.

Mr Nnaji dai tafe dsa takardar kuka da kuma damuwa wadda aka rubuta ma Shugaban kasa Buhari, sun nemi da gwamnatin tarayya ta kawo dauki, akan yadda ake yi ma ‘yan    kasuwa ‘yan  asalin Nijeriya.

“Abin ban takaici ranar Asabar 22 ga watan Satumba daya daga cikin mambobin da suke mata gudea hudu, Mrs Stella Ogonna Okpaleke wadda aka kulla shagunanta, da hukumomin Ghana suka yi ta kasahe kanta”.

“Ta kashe kan nata na saboda sahgon ta da kuma na mijinta wadanda aka rufe, labarin kuma da muka ji da hakan  ta faru, sai al;’amaru suka jagule mata ta rasa yadda zata yi”.

“Ita tana daga karamar hukumar Nnewi ta jihar Anambra bamu kuma san ko nawa bane ake binta bashi, amma kuma mun sami labarin cewar ta dauki bashi ne saboda ta bunkasa kasuwancin ta.” kamar dai yadda shugaban  kungiyar ya bayyana.

Ya dai ci gaban da bayanin cewar irin cin mutuncin da ake yi ma ‘yan Nijeriya mazauna birni Kumasi abin ba bu dadi.

“Abin da akwai takaici idan aka yi la’akari da yadda ita matar ta kashe kanta ne, don haka ya yi kira ga Shugaban kasa Buhari da yayi sauri ya dauki mataki, saboda a kauce ma sake aukuwar irin haka nan gaba.

Ya ce, ‘yan kasuwar Nijeriya mazauna Ghana ana yi masu wulakanci da hukumomin kasar Ghana ke yi ma su.

A nata jawabin Mrs Dabiri- Erewa ta mika gaisuwar gwamnatin tarayya zuwa ga ‘yan kungiyar da kuma iyalan wadda da mutu.

Ta yi kira ga mambobin da cewar su yi hakuri ta kuma basu tabbacin cewar Shugaban kasa zai kawo dauki da kuma daukar mataki dangane da al’amarin , za kuma a samo maslahan shi al’amarin.

“Yanzu na fara baku hakuri na san al’amarin yana da zafi da kuma ban tausayi, abin da kwai takaici, amma ina kira gare ku da kuyi hakuri”.

“Na yi kira gareku da cewar da ku yi hakuri Allah ya jikanta ya kuma sa ta huta”.

“Idan an kusa rufeb ta ya dace ku fada mana saboda mu aika mata da sakon ta’aziyya

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya bada rahoton cewar ‘yankasuwar Nijeriya mazauna kasar Ghana, yanzu ba dadin harkar kasuwanci suke ji ba, idan aka yi la’akari da dokar fidda mutane daga shagunan su ta watan Yuli  27.

Hukumomin kasar Ghana suna bukatar cewar ‘yan kasuwa zasu biya dala milyan daya, a matsayin mafi karancin jarin da ake kukata saboda ayi harkokin kasuwanci a kasar Ghana, kamar dai yadda aka bayyana a dokar da ma’aikatar kasuwanci da ma’aikatu ta shekarar 2013 ta bayyana.

Advertisement
Click to comment

labarai