Kwankwaso Na Barazanar Fice Wa Daga PDP — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Kwankwaso Na Barazanar Fice Wa Daga PDP

Published

on


Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi barazanar fice wa daga jam’iyyar PDP matukar uwar jam’iyyar ta kasa ta kuskura ta cire mambobin Kwankwasiyya daga cikin jerin ‘yan takara.

In dai za a iya tuna wa Kwankwaso ya gudanar da zabensa na fid da gwani a matakai daban-daban. Majiyarmu ta shaida mana cewa Kwankwason ya bayyana hakan ne a lokacin zaman tattaunar da suka yi a Legacy House da ke  Abuja.

Tattaunawar ta samu halartar manyan ‘yan jam’iyyar  irin su, Bello Hayatu Gwarzo da Ambasada Aminu Wali da sauran su.

Majiayar ta mu ta ci gaba da shaida mana cewa, an shirya taron ne domin a sake duba sunayen ‘yan takarar jam’iyyar daga jihar Kano.

Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa wanda shi ma ke da nasa bangaren a jam’iyyar ta PDP shi ya yi nasa zaben fid da gwanin.

Majiyar ta mu ta ce, sakamakon wannan sabanin ne Kwankwaso ya sha alwashin cewa matukar ba ayi la’akari da ‘yan takararsa ba, to akwai yiwuwar ya fice daga jam’iyyar ta PDP.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!