Ahmad Musa Ya Mayarwa Da Kociyan Libiya Martani — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ahmad Musa Ya Mayarwa Da Kociyan Libiya Martani

Published

on


Dan wasan gaba na Super Eagles ta Najeriya dan kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr dake kasar Saudiyya, Ahmad Musa, ya bayyana cewa zasu mayarwa da kociyan kasar Libya martini bisa kalaman da yayi na cewa kasashen Africa ta yamma sun yadda da tsafi a kwallon kafa yayinda kuma kasashe Arewacin Africa suka dogara da Allah.

Wannan kalamai sun jawo cece kuce sosai wanda har sai da takai daga baya kociyan na Libya wanda ya ajiye aikinsa a shekaran jiya ya fito ya bayar da hakuri bisa kalaman nasa da yayi akan bakar fatan Africa

Duk da cewa ya fito ya bawa duniya hakuri, Ahmad Musa, wanda ake saran shine zai zama kyaftin din tawagar ta Najeriya a yau ya bayyana cewa zasu bashi amsa amma sai acikin filin wasa

“Ban damu da abinda yafada ba saboda bashi da amfani a wajena a matsayina na dan wasa sai dai zamu mayar masa da martani acikin filin wasa duk da cewa ya ajiye aikin koyar da ‘yan wasan kasar” in ji Ahmad

Ya kara da cewa Yanzu aikin da yake gabansu shine samun nasara a wasan domin ganin sun kai kasar nan gasar cin kofin nahiyar Africa da kamaru zata karbi bakunci saboda yakamata ace Najeria taje gasar.

A yau ne dai Najeriya zata fafata wasa da kasar Libya a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa da za’a fafata a kasar Kamaru a shekara mai zuwa

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!