Amfanin Bishiyar Gamji A Jikin Dan’adam — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIWON LAFIYA

Amfanin Bishiyar Gamji A Jikin Dan’adam

Published

on


Gamji wata bishiya ce da ke da tsayi da tarin ganye mai duhu a jikinta wadda ba ta girma a cikin gidaje, asali a cikin daji ake samun ta a wasu yankuna na Arewaci da kuma Gabascin Nijeriya. Bishiyar gamji tana da ban tsoro domin matattara ce ta Aljannu kuma waje ne na aikata miyagun ayyuka masu nasaba da sihiri da tsafe-tsafe da sauran ayyuka mugayen matsibbata. A lokuta da dama za ka tasarwa bishiyar gamji don samo wani abu a jikinta domin yin magani amma kafin ka isa ga bishiyar, nan take a kan iya firgitaka da wani abin tsoro. Wasu ma a kan shafe su da mari ko a biyo su ana duka ba tare da ganin ainihin kowa ba musamman idan aka je a tsakiyar rana ko aka je da manufar aikata wani mugun aiki a wajen. Domin haka ana tasarwa bishiyar gamji a kan yi wadansu addu’oi kevavvu don gudun vacin rana.

Ko masu maganin gargajiya ba a haka kawai suke debo bishiyar ba, suna da dabaru daban-daban da suke bi su samo kusan dukkanin abin da suke bukata a kanta. Bishiya ce da a lokuta da dama ana iya dauko iskoki a wajenta. Bishiya ce da ba abarin yara su yi wasa a karkashinta dan gudun tozali da miyagun jinnu. Bishiya ce da idan ka ce za ka farka daga barci a cikin tsakiyar dare ka je ka sassako vawanta ko gino saiwarta to za ka iya gamuwa da tirjiya ta ban tsoro ko kuma ka haukace. Bishiya ce da idan aka ci karo da vacin rai za ka je wajen sassako vawanta kana fara sarawa sai ka ga jini ya zubo kai mutum dole hankalinka ya tashi. Bishiya ce da ba a bukatar mutum mai jinnu ko alamun jinnu a jiki walau mace ko namiji ya ziyarta dan koda sun kwanta wani abun na daban zai iya faruwa. Bishiya ce da ana saranta ana sassaka amma kuma tofo take yi wannan ne ya sa masu karin magana a Hausa ke cewa ‘sara da sassaka baya hana gamji tofo’. Akwai ma wasu kwari da macizzan da ba sa zama a ko ina sai a kogon bishiyar gamji. Wannan duka dai yana da alaka da iskokai.

A tsarin maganin gargajiya na kasar Hausa, an jima ana amfani da gamji kama daga ganyen bishiyar, vawanta, itatuwanta da kuma sayyunta dan yin maganin wasu dai-daikun cututtuka da wasu asirrai da kuma fa’idodi. Wasu masu ba da maganin gargajiya a Sokoto da Argungu dake a jihar kebbi suna amfani da ganye ko diyar bishiyar gamji dan maganin rashin haihuwa a tsakanin maza da mata.

–   Ana amfani da bishiyar gamji dan maganin farfadiya.

–   Ana amfani da gamji dan maganin mafarkin fitsarin kwance.

–   Ana amfani da gamji dan warkar da masu rashin lafiyar tavin hankali.

–   Mutanen dake a yankin Tenda suna shafa garin vawan gamji kamar man shafi a goshi dan warkar da ciwon kai na vangare daya.

–   A gabascin Afrika ana save vawon gamji danyen sa sai a tace da ruwan dumi a sha rabin kofi bayan an karya dan maganin cututtukan ciki.

–   A yankin jamhuriyar Afrika ta tsakiya wato central African republic, ana tafasa vawon gamji sai a marmasa gishiri a dunga wanke baki da ruwan tun da safe dan maganin amosanin baki da ciwon hakora da kuma jinin dake zuba daga baki.

–   A kasar Senegal ana digawa jinjirai man bishiyar gamji a ido dan magance cututtukan idanu.

–   A kasar Zimbabwe ana markada gamji sai a diga kamar matse ga idanuwa dan magance komtsan ido.

–   A kasar Cotedivoire suna matse ta sai su yi amfani da ruwan da aka markado daga ganyen gamji su maida shi man shafawa dake rage radadi ko zafin ciwo ga tomashe ko targade.

–   Ana hada saiwar kirya da ta bishiyar manguro da kuma saiwar gamji a tafasa a rinka zama a ciki dan maganin basir mai tsiro.

–   Bishiyar gamji na maganin kambun baka da maita.

–   Ta na maganin yawan damuwa da kuma rashin bacci.

Allah ya ba mu ikon gwada wa tare da samun lafiya.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!