Fara Sharar Gonar Da Dangote Zai Kamfanin Suga Ya Kawo Rudani A Akoh — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Fara Sharar Gonar Da Dangote Zai Kamfanin Suga Ya Kawo Rudani A Akoh

Published

on


Alumman kauyen Akoh sun fashe da kuka sakamakon yadda Motochin rusau suk maida kauyensu gonan rake. Tun a shekarar da ta gabata ne hamshakin Dan kasuwar nan Alhaji Aliko Dangote  ya kuduri aniyar samar da katafaren gonan rake da za a rika yin suga  a Jihar Nasarawa.

Tuni Gwamnatin Jihar Nasarawa ta mika yanki  Tunga da ke karamar hukumar Awe, don yin wannan aiki saboda guri ne da ke da danshin fadama inda kuma ya dace da noman rake.

Attajirin ya amince tunda ya ga wanan gurin inda aka yi yarjejeniyar biyan mazauna wanan gurin hakkokinsu na gonakansu da gidaje da ke wajen.

Da yake zanta wa da manema labarai shugaban al’umma mazauna kauyen Akoh Mista Zaki Mchainan Alebo ya ce; “Kwatsam mun ga motar rusau ta shigo garinmu da rana tsaka ,  ba tare da sanin me ke faruwa ba ta soma rusa gidajenmu da gonakanmu ba tare da sun sanar damu cewa ga abin da ya kawo su ba. Koda yaranmu suka yi magana sai jami’an tsaro suka kama su da duka suka daure su.

Motar ta rusa gidajenmu ba su bari mu kwashe kayayakinmu ba hatta amfanin gonarmu da muka tara su guri daya an bajesu tare da wadanda ba su yi ba duk an yi mana asara “

Ya kara da cewa ni ban san dalilin yin haka ba  sai daga baya aka sanar da mu cewa wai  Dangote ne ya sayi  wajen kuma an biya mu. Ya kara da cewa, shi fa  bai san da wanan magana ba. Babu wanda ya taba sanar da shi makamancin wanan magana cewa Dangote ya sayi garinmu kuma anbiya mu.

Zaki ya ce; Shekararsa sun kusa 90 a nan kauyen aka haife shi ai ko babu komai suna da hakkin a sanar da su ga halin da ake ciki. Amma rana tsaka a rusa wa mutum gida asa wuta a kona komai ba a bari ya dauka komai ba.

Shi ma Shugaban matasan Kabilar Tb na jihar Nasarawa Mista Piter  Ahmba ya ce;  wannan abin da ya faru abin tausayi ne saboda halin da al’umman kauyen Akoh suke ciki yanzu dole a tausaya musu. Saboda suna kwana a waje sakamakon an rusa masu gidaje amfanin gunarsu an lalata an kona kauyen an sare itatuwa.

Ya ce, wanan abin da gwamnatin Nasarawa da Dangote suka yi bai dace ba an yi wa al’umma barnar miliyoyin Nairori.

Shi ma da ya ke jawabi a madadin Kamfanin Dangote  mai magana da yawun kamfanin Alhaji Sa’idu Muhammad ya ce; sun samu izini ne daga gwamnatin jihar Nasarawa da kuma mai Martaba Sarkin Tuna Muhammad Ibrahim Shu’aibu. Su ne ke da alaka da kamfanin saboda da su suka yi magana kuma suka samu izini.

Amma Sarkin na Tunga Alhaji Muhammad Ibrahim ya ce ; shi bai san da wanan aika-aikan ba, wanan abin da aka yi bai dace ba.

Tuni ‘yan siyasan Jihar Nasarawa suke ta tofa albarkacin bakinsu game da yunkurin sayar da jihar ga hanshakin Dan kasuwan saboda mallake albarkatun jihar.

Faruwan wanan lamarin ya sanya al’umman jihar suke ganin aikata irin wannan aiki da Kamfanin ya yi a garin Akoh ba daidai ba ne.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!