Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Wa Mutum 50 Takunkumin Hana Fita Waje — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Wa Mutum 50 Takunkumin Hana Fita Waje

Published

on


Gwamnatin tarayya ta sanya sunayen wasu mutum 50 a jerin sunayen wadanda ta haramta wa fita daga kasar nan, rahotanni sun nun duk cikar mutanen manyan ‘yan siyasa ne.

Mataimakin shugaban kasa na musamman bangaren yada labaru, wato Malam Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar a yau Asabar, bayan da wata kotu ta tabbatar da dokar da ta baiwa shugaban kasa damar kwace kadarorin da ake zargin na sata ne.

An umarci hukumomi masu sanya idanu kan shige da fice da su amshi takardun duk wadanda sunayensu yake a cikin wannan jerin sunayen, har sai an kammala bincike akansu.

A cikin dokar duk wata kadara da ta kai Naira miliyan 50 ba za a bari wanda sunansa yake jerin sunayen ya yi tahamulli da ita ba, har sai kotu ta tabbatar da halarcin wannan kadarar.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!