Na Je Gidan Obasanjo Ne Domin Yin Sulhu Tsakanisa Da Atiku- Shaikh Gumi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Na Je Gidan Obasanjo Ne Domin Yin Sulhu Tsakanisa Da Atiku- Shaikh Gumi

Published

on


Shahararren malamin addinin Musulincin nan da ke zaune a garin Kaduna, Shaikh Dakta Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana cewa, ya je gidan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne domin ya  daidaita tsakanin ta tsakanin tsohon shugaban kasar da tsohon mataimakinsa bisa sabanin da suka samu a baya.

Sheikh Gumi ya tafi tare da wani shahararren malamin addinin Kiristanci ne Bishop na cocin Katolik Dioces da ke Sakkwato Rabaran  Mathew Hassan Kukah inda suka yi ganawar sirrin a dakin karatun na Obasanjo da ke gidansa a garin Abeokuta, ta jihar Ogun a shekaranjiya Alhamis.

Da yake magana da wakilinmu ta wayar tarho jim kadan bayan dawowarsa gida daga taron Shaikh Gumu ya ce Rabaran kukah ne ya gayyace shi, domin ya zama shaida wajen yin sulhun..

Haka kuma ya ci gaba da cewa Kukah ya sha tuntubar manyan mutanen da ke kasar nan domin su shiga tsakini na daidaita tsakanin Obasanjo da Atiku domin a samu kwanciyar hankali a tsakani.

“A matsayina na malamin addini dole ne in wuce gaba wajen yin sulhu, musamman inda aka bukaci in shiga domin samar da zaman lafiya da walwala atsakanin al’umma.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!