2019: Ya Dace ’Yan Nijeriya Su Sake Yin ‘APC Sak’ – Musa Sani — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

2019: Ya Dace ’Yan Nijeriya Su Sake Yin ‘APC Sak’ – Musa Sani

Published

on


Kasa da watanni biyar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara gudanar da zabubbukan sabbin shugabannin da za su jogaranci al’ummar kasar nan na tsawon shekaru hudu masu zuwa, an bukaci al’ummar kasar nan da su sake mara wa Jam’iyyar APC mai mulki baya ta hanyar yin ‘sak’ a zaben shugabanninsu a dukkan matakan mukaman siyasa.

Daya daga cikin Dattaban da ke kishin ganin mulkin dimukuradiyya ya dore a kasar nan kuma daya daga masoya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Musa Muhammad Sani Yandota Jos, ne ya yi wannan kira a lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa bisa cika shekara Hamsin da Takwas, da samun mulkin kan kasar nan a tattaunawar da ya yi da wakilimma a Jos babban birinin jihar Filato, ranar Larabar da ta gabata.

Ya yaba bisa nasarorin da shugabannin da suka ja ragamar mulkin kasar nan suka samu wajen inganta tattalin arziki kasa da na rayuwar al’umma. A cewarsa, dukkan shugabannin da suka ja ragamar mulkin kasar nan karkashin mulkin soja da na farin hula duk sun sami nasar dora tubalin ginin kasar don yanzu idan ka duba al’ummar kasar nan sun sami yalwar rayuwa idan aka kwatanta da baya kafin samun ‘yanci.

Ya yi misali da cewa a yanzu mace-macen kananan yara da munanan cututtukan da ke kashe al’umma ya ragu idan aka kwatanta da baya kuma arziki ya bunkasa a tsakanin mutane.

“Yanzu za ka ga magidanci ya haifi yara sama da Talatin kuma sai ka samu dukkansu sun rayu wanda a wadace kuma mawuyaci ne a sami hakan a baya. Haka nan kuma shugabannin sun yi nasarar gina manyan hanyoyin mota da samar da irin shuka na zamani da wadata manoma da takin zamani da Turaktocin Noma. Hakan ya sauwake wa manoma wajen aikin noma”, in ji shi.

Da yake kwatanta mulkin farin-hula da na soja a gwamnatoci daban-daban da aka yi a kasar nan tun samun yancinta a Alib 1960, Alhaji Sani ya ce ko kadan ba hadi tsakanin mulkin farin hula da na soja. Ya ce mulkin farin hula ya fi dacewa da a rika gudanarwa a kasar nan saboda in ji shi mulkin farin hula yafi baiwa ‘yan kasar yanci fadin albarkacin bakinsu walau ta yin yabo ko suka. Kuma ya ce yana baiwa yan kasar damar a dama da su a harkar gudanar da mulkin kasar daga kowani bangare na kasar suke.

Haka nan kuma ya yaba bisa nasarar da gwamnati mai ci yanzu karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta samu a cikin yan shekaru uku da rabi din nan da ta yi da fara jan ragamar kasar. Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari, ya sami nasara wajen hada kan al’ummar kasar nan, kana ya ce yanzu nuna banbancin addini da na kabilanci ya ragu da kashi saba’in cikin dari idan aka kwatanta da lokacin tsohuwar gwamnati ta Good-Luk Ebele Jonathan.

Ya kara da cewa, “Wannan gwamnati mai ci yanzu karshin jagorancinsa ta sami nasarar kakkabe  ‘yan Boko-Haram a dukkan yankunan da  suka kame a jihohin Arewa maso Gabas, hakanan shugaban kasar ya yi nasarar sauya tsarin tattalin arzikin kasar nan. Cin hanci da rashawa ya ragu ainun a cibiyoyin gwamnati”, sai yaroki al’ummar kasar da su binne banbancin siyasa, addini da kabilanci dake sakaninsu su hada kansu su zama sinsiya madaurinki daya su sake zaben jam’iyyar APC, daga matakin gwamnatin tarayya zuwa na kananan hukumomi a zabubbukan da za a yi a Alib 2019.

Ya zargi ‘yan siyasan da suke sauya sheka daga wannan jam’iyyar zuwa wancan da nuna son kai da rashin kaunar cigaban talakokin kasar ya yi misali da dan takarar jam’iyyar PDP,Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya bar jam’iyyar APC, ya koma PDP, don kwadayin ya yi mulki kawai ba don kishin kasar ba.

Alhaji  Sani ‘Yandoya Jos, hakanan ya yaba da irin salon mulkin da gwamnan jihar Filato Barista Simon Bako Lalong ke gudanarwa a jihar, inda ya ce “tun da Gwamnan ya dare kan karagar mulkin jihar fadace-fadace, da zub da jinin Dan Adam ya ragu a jihar, idan aka kwatanta da baya kafin ya kama mulkikn jihar. Ina iya tunawa a gwamnatin da ta gabata akwai lokutan da suka rika binne gawawwakin mutane 362, 120, 70, a lokuta daban-daban a jerin rikece-rikicen da akayi a baya a jihar. Amma tun da Gwamna ya kama ragamar mulkin jihar fadace-fadace ya ragu inb a na baya-bayan nan da ya tashi a garin Jos da wanda yake furuwa lokaci-lokacin a tsakanin Fulani makiya’ya da manoma da ake samu a wadansu kananan hukumomin jihar ba”.

Alhaji Sani ‘Yandoya Jos, ya yi Allah wadai da aukuwar rikicin Jos, kana ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga Filani Makiya’ya da Al’ummomin kananan hukumomin da ake fama da irin wadannnan fadace-fadacen da su ji tsoron Allah su dai na kashe mautanen dabasu san hawa ba bare sauka.

Ya nemi da su binne duk wani bambancin da ke tsakaninsu su dawo su hada kai kamar yanda iyayensu da kakaninsu suka zauna a baya don a baiwa kowa damar ba da tasa gudumar wajen gina jihar da kasa baki daya.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!