Barista Abdul-Ganiy Ne Dan Takarar Gwamnan PRP A Gombe — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Barista Abdul-Ganiy Ne Dan Takarar Gwamnan PRP A Gombe

Published

on


A lokacin da babban zaben shekara ta 2019 ke ta kara karatowa jamiyyar PRP ta tsayar da babban Lauya Abdul-ganiy M Bello ya zama dan takarar ta na gwamna a jihar Gombe.

Da yake zantawa da manama labarai kwanaki bayan taron jamiyyar tasu Barista Abdul-ganiy M Bello yace jamiyyar ce taga dacewar sa ta amince masa da ya zama mata dan takarar gwamna dan shi ne zai iya karawa da sauran manyan jamiyyun a jihar duk da acewar shi jamiyyar su ba karama bace.

Barista Abdul-ganiy yace idan yaci zabe ajandodi uku zai bai wa kula sosai dan kar ya dauka suyi yawa su zama matsala ajandodin kuma sune yaki da talauci da rashin da’a da jahilci sannan kuma zai inganta harkar ilimi.

Ya ce jami’yyar PRP ita ce jamiyyar talakawa da Malam Aminu Kano da wasu jajirtattun yan Najeriya suka kafa ta tun a shekarar 1978 kaga ita ce jamiyyar da ta girmi duk wata jam’iyya a kasar nan.

Daga nan sai dan takarar gwamnan ya kara da cewa idan har a ka zabe shi ya zama gwamna a jihar Gombe zai yi dukkan mai yiwuwa na ganin ya cika alkawuran da ya dauka wa jama’ar jihar Gombe.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!