Burina Shi Ne Na Zama Babbar Marubuciya – Aisha Turaki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Burina Shi Ne Na Zama Babbar Marubuciya – Aisha Turaki

Published

on


Shahararriyar marubuciyar nan ta yanar gizo (online writer) AISHA MUHAMMAD TURAKI, wadda aka fi sani da Kueen Nerdy Turakee, wato marubuciyar fitaccen littafin nan mai suna ‘Alkawarin Mutuwa’ da kuma ‘Hamshakiya’ sun tattauna da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, ADAMU YUSUF INDABO. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Farko dai masu karatu za su so ki fara gabatar mu su da kanki.

To da farko dai sunana Aisha Muhammad Turakee wadda a ka fi sani da Kueen Nerdiya Turakee.

 

Tarihin rayuwarki fa?

Da farko dai mahaifina dan asalin garin Borno ne yaren Bariri, Mamana kuma Shuwa Arab ce, mu na zaune a jahar Kano inda aiki ya dawo da mahaifina Kano. An haife ni a Kano ranar 16 June 1996. Na yi karatuna na nursery da primary anan Iman nursery,primary and secondary school kafin na fara Abu Hanifa Academy tun daga JS1 zuwa SS3. Yanzu kuma alhamdulillah na gama karatuna na karanci biochemistry a Federal College Of Education Kano. Bayan haka na yi makarantar Islamiyya har ma na yi sauka tun ina JS 3.

 

Yanzu sai aiki ke nan ko kuma aure?

(Murmushi) Kowanne ya fara zuwa ina maraba da shi. Domin lamarina na mikawa Madaukakin Sarki don ya zaba min abun da ya fi alkhairi gare ni da rayuwata da kuma mutuncina.

 

To wanne tsani kika taka ya kai ki duniyar rubutu da marubuta?

Gaskiya kafin in fara rubutu ban sha wani wahala ba saboda na hadu da kungiya masu mutunci da kara da kuma kaunar juna, don haka ba abin da zance wa Allah sai godiya.

 

Wacce kungiya ke nan?

Kungiyar ELOKUENCE WRITERS ASSOCIATION wacce fitacciyar kuniya ce da ta ke online.

 

Wasu marubutan kafin su fara rubutu da makaranta ne, shin ko ke ma kin yi karance-karancen littattafan Hausa ne ko kuma littattafan online kafin ki fara rubutu?

Gaskiya na dade ina karatu tun ina primary lokacin Mamana da Babana har zane ni suke yi ko su yaga littafin saboda karatun da nake yi fa da gaske nake yi ba dare ba rana sai ka ce ibada, amma a karshe suka hakura na ci gaba  har a online.

 

Mun ji kin yi karance-karancen littafan Hausa tun kina karama, to cikin marubutan waye ko wace gwanarki?

Gwanayena a cikin marubuta su ne: Halima Abdullahi K/Mashi da kuma Sumayya Abdulkadir.

 

To yaushe ke ki ka fara yin rubutu?

Gaskiya ban dade sosai ba, don ban rufa shekaru Biyu da farawa ba.

 

Wanne ne littafinki na farko da kika fara  rubutawa?

Hamshakiya shi ne littafin da na fara rubutawa.

 

Littafin HAMSHAKIYA a kan me yake yin magana?

Littafin Hamshakiya kukan kurciya ne a kan kada ka wulakanta mutum saboda ka gan shi a cikin wani yanayi na kaskanci, saboda dan adam halittar Ubangiji ce mafi kyawu da kuma daraja, bayan haka ganin mutum a kaskance ba yana nufin matsiyaci ba ne tana iya yuwuwa arzikin mutumin ma kake ci. Sannan littafin Hamshakiya na tabbatar da cewa zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzuru ko ana shaho sai ya yi, saboda sara da sassaka ba ya hana gamji tofo.

 

Zuwa yanzu kin rubuta littattafai guda nawa?

A cikin shekaru Biyu da fara rubutuna na rubuta littattafai guda shida, Hamshakiya, Alkawarin Mutuwa, Son Zuciya, Dr. Suhaima, A Daren Sallah, Waye Zabina?

 

Cikin wadannan littafai guda Shida, wannne ya fi karbuwa a wajen makaranta?

Alhamdulillah kowanne ya samu karbuwa amman dai Alkawarin Mutuwa ya fi sauran karbuwa.

 

To wanne ya fi ba ki wahala wajen rubutawa?

Alkawarin Mutuwa din dai, saboda na yi rubutun ne a kan tsafi wanda ke tare da abubuwan ban tsorososai, to a lokacin ina rubutawa ina jin tsoron kada fa ya zo ya faru a gaske, don haka sai na tsinci kaina cikin zulumi da fargaba da kuma tararradi, hakan ya sa sai dakyar na iya karasa rubutawa, shi ma ba don azalzalar makaranta ba da suke bibiyar labarin saboda ya musu dadi wata kila da har yau ban kammala shi ba.

 

To ke me ya kai ki rubutu a kan tsafi alhalin ana ga mata sun fi karkata ga rubutun soyayya?

Ai rubutun soyayyar ne kullum shi ake yi babu sauyi, don haka ya gundiri makaranta suna bukatar canji, shi ya sa na canja salon rubutun.

 

A fagen marubuta kina da ubangida ne ko malami da yake duba labarinki ko ba ki shawara ko kuma kina aikinki ne ke kadai?

Gaskiya nice boss din kaina, sai kuma in na tura group in da gyara a gyara min, haka makaranta ma wani lokacin sukan zo da shawarwarin da ba a rasa ba.

 

Kasancewarki marubuciya a yanar gizo,   shin ko kina da burin nan gaba ki buga littafi?

Eh, in sha Allah ina da burin buga littafi.

 

Mene ne ra’ayinki game da rubutun fim?

Gaskiya ba ni da ra’ayi a kan rubutun fim.

 

Kin taba shiga gasar rubutu?

Gaskiya ban taba shiga gasa ba sai dai ko nan gaba.

 

A cikin yan uwanki marubuta, kina da amini ko aminiya da koyaushe za a iya jin labarinki ko halin da kike ciki daga wajen ta, in da akwai to waye ko kuma wace?

Eh, akwai su ba ma Daya ba, farko akwai Madeena Usman, marubuciyar littafin Hanta Da Jini da Na’ira Daughter ita ma marubuciya ce, sannan Muhiebert India marubuciyar Sirrin Boye, dukkan membobinmu ne na kungiyar Elokuence Writers.

 

A rayuwarki me kika fi so, kuma me kika fi tsana?

Ina son zaman lafiya kuma na tsani tashin hankali.

 

Me ne babban burinki a rayuwa?

Burina shi ne in zama babbar marubuciya.

 

‘Yan uwanki marubuta, wanne kira za ki yi gare su?

Kirana gare su shi ne don Allah mu hada kanmu, mu zama tsintsiya madaurin ki daya, duk wanda ya yi kuskure mu ringa kokari muna gyara masa tare da karfafa masa gwiwa.

 

Me za ki fadawa maasoyanki da koyaushe suke bibiyar rubutunki?

Masoyan labaraina masoyana ne, don haka ina kaunar su a  duk inda su ke, ina musu fatan alkhairi kamar yadda su ma suke yi min, kuma ina godiya da yabawa sosai da sosai. Allah ya bar zumunci da kaunar juna Ameen.

 

To Malama Aisha mun gode.

Ni ma na gode.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!