Shin PDP Za Ta Iya Dawo Wa Mulkin Najeriya A 2019? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Shin PDP Za Ta Iya Dawo Wa Mulkin Najeriya A 2019?

Published

on


A Karshen makon jiya ranar Lahadi, 7 ga Okotoba, 2018, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, wato PDP, ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, takarar shugabancin kasar a babban zabe na tafe da za a gudanar a cikin watan Fabrairu na shekara ta 2019.

Tun daga lokacin da PDP ta tsayar da shi takara a ka ga yadda jam’iyya mai mulkin kasar, wato APC, ta ke ta faman zungurinsa tare da kai ma sa farmaki irin na siyasa, haka nan kuma magoya bayan jam’iyyar su ma ba a bar su a baya ba, inda su ke ta yunkurin tunatar da ’yan kasa da masu kada kuri’a irin munanan abubuwan da a ke zargin Atikun da aikatawa, musamman a lokacin da ya ke rike da mukaminsa na mataimakin shugaban kasa a lokacin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Bugu da kari, su na ta yayatawa tare da habaici kan zargin yin amfani da dukiya wajen samun kuri’un deliget din PDP a lokacin babban taron jam’iyyar da a ka gudanar a garin Fatakwal, inda a ka zabo Atikun a matsayin dan takarar PDP din.

A bangaren PDP da Atiku ba a bar su a baya ba wajen mayar da martani ta hanyar karyata wadancan zarge-zarge da kuma fito da guraren da su ka zargin gwamnatin APC ta gaza cimma nasara a mulkinta.

Hakika yanayin yadda APC da fadar shugaban kasa su ka fito karara su na sukar takarar Atikun ya na nuna cewa, lallai PDP ta tsayar da kwakkwaran dan takara, wanda idan APC din ba ta tashi-tsaye ba, za ta iya shan mamaki a babban zaben na 2019.

Babban abin tsoron da Atiku ya ke da shi shi ne tsananin gogayya da kwarewa ta fuskar siyasa, wanda a fili ta ke cewa, ya sha kan ban garen dan takarar APC, wato shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari, a wannan fanni a siyasance.

Hatta tsayar da Atikun da PDP ta yi, kafin a tafi gangamin fitar da gwanin, wasu gani su ke yi ba zai kai labari ba, amma yanayin yadda ya nuna gogewa a siyasance sai ya ba shi nasarar da ya ke nema a taron. A fili ta ke cewa, ko da akwai tasirin kudi, to akwai kuma gogewa, domin mafi yawan wadanda ya yi takarar da su su ma su na da kudin, wasunsu ma a cikin gwamnati su ke tsundum su na damawa.

Masu nazari ke ganin cewa, idan har da gaske ne Atiku ya yi amfani da kudi a taron gangamin PDP na kasa, to la shakka kudi na iya yin tasirin a babban zaben kasar idan a ka yi la’akari da yadda talakan Najeriya ya ke jan kari, saboda yanayin manufofin tattalin arziki na gwamnatin APC a karkashin jagorancin Shugaba Buhari.

Bugu da kari, tarihi ya nuna cewa, Buhari bai taba kayar da dan takarar Arewa a babban zaben kasa ba, har ma wasu nna ganin cewa, ya yi nasara a kan tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a 2015 ne, saboda kasancewarsa ba dan Arewa ba. A yanzu kuwa da Atiku Abubakar zai gwabza, wanda cikakken dan Arewa ne kuma mai kyakkyawar alaka da ’yan Kudu.

Wani dalilin da ke skara bai wa PDP kwarin gwiwa kuma shi ne, yadda yawancin tsofaffin jagororin kasar, musamman sojoji, su ka fito su ka goyi da bayan takarar Atikun. Haka nan kuma sauran ’yan takarar da ya kayar su ma sun taya shi murna kuma sun yi alkawarin taya shi yakin neman zabe, sabanin abinda a ka yi tsammani tun da faru na cewa, wasu daga ciki za su iya yi ma sa tawaye.

Irin dagiyar da Atiku ya ke da ita tare da jajircewa kan dukkan abinda ya saka a gaba, wasu dalilai ne da ka iya ba shi nasara a babban zaben na 2019. Sannan kuma zai iya yin amfani ya samu dama kan yadda farin jinin shugaban kasa Buhari ya ragu tun bayan darewarsa gadon mulkin Najeriya a 2015.

To, amma saidai ita kuma PDP a kan kanta tare da wasu manyan matsaloli, wadanda talakan Najeriya ya ki ya mance da su. Daya daga ciki shi ne yadda jam’iyyar ta kwashe shekaru 16 ta na mulkin kasar ba tare da ta iya ciyar da ita gaba; karewa ma a na alakanta yawancin matsalolin da a yanzu Najeriya ke ciki da irin rikon sakainar kashin da PDP ta yi ma ta a cikin shekara 16 din can.

Cin hanci da rashawa karara sun yawaita a zamanin PDP, baya ga kuma dimbin satar dukiyar gwamnati da a ke zargin jami’ai da ’yan siyasa ke yi ba ji ba gani.

Shi kansa dan takarar na PDP, wato Atiku Abubakar, mafi yawa su na yi ma sa kallon a matsayin wanda idan ya kafa gwamnati zai iya karfafa wadancan munanun dabi’u na karfafa cin hanci da rashawa, siyasar ubangida da kuma satar dukiyar gwamnati.

Tabbas wadannan lam’o’i na iya kawo wa PDO cikas a lokacin zaben. To, amma ita kuma APC ta sake talaka ya ji a jikinsa da yawa ta yadda ya kai munzali irin na mutumin da ya fada a cikin ruwa, wanda masu iya magana ke cewa ko takobi a ka mika ma sa kamawa zai yi.

Koma dai mene ne, lokaci ne zai zama raba-gardama!

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!