Kama Dino Muka Je, Ba Kashe Shi Ba  –’Yan Sanda — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kama Dino Muka Je, Ba Kashe Shi Ba  –’Yan Sanda

Published

on


Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da cewar ta aike da jami’anta zuwa gidan Sanata Dino Melaye da ke Aiyetoro-Gbede a cikin jihar Kogi domin kewaye gidan hadi da cafko shi a ranar 11 ga Oktoba, cafkowar da bai samu nasarar iyuwa musu ba.

A cikin wata sanarwa daga ‘yan sandan wanda ta rabar a garin Lokoja ta shaida cewar daukan wannan matakin yana da alaka ne da harbin wani jami’inta Sajen Danjuma Salisu da aka yi a ranar 19 ga watan July wanda ake zargin wasu ‘yan daba wasu yi wa Sanatan biyayya ne suka aikata hakan.

Sanarwar dauke da sanya hanun Kakakin rundunar, DSP William Aya, ya fayyace zargin da Dino Melaye ya yi a shafinsa na twitter inda ke zargin cewar ADC din gwamna Yahaya Bello ya jagoranci wasu jami’an ‘yan sanda da nufin su hallakashi a gidansa.

Ya ce; “Babu wani abun da ADC ya yi a kan wannan kes din. Don haka, rundunar ‘yan sanda tana son ta sanar da jama’a cewar wannan ba ma kawai yarfen siyasa ba ce, a’a karya ce tsuki tamallece Sanatan ya sharara kawai.

“shugaban ‘yan sandan ‘kwamishina’ ya tura jami’an ‘yan sanda da su cafko Dino a gidansa, amma cikin tsautsayi sai ba mu cimmasa ba a cikin gidansa,” inji sanarwar

Ya zargi Melaye wanda sanata ne da ke wakiltar mazabar Kogi ta yamma da shirya ‘yan daba wadanda suka kai hari wa jami’an tsaro a daidai lokacin da suke gudanar da aikinsu a daidai Mopa-Aiyetoro-Gbede a ranar 19 ga July ba tare da wani dalili ba.

“Yan daban sun harbi wani jami’i mai lambar aiki No. 432913, mai suna Sgt Danjuma Salisu, wanda a yanzu haka yake kan amsar kulawar likitoci a asibitin Beda Crest Hospital, da ke Abuja,” Inji ‘yan sandan.

Aya ya shaida cewar ‘yan sanda sun bukaci Melaye ya bayyana a gabansu ta wata wasika mai kano kamar haka No AR:3000/KGS/D/BOL.43/670, da ke da kwanan wata 23/7/2018, amma ya ki amsar gayyatar da aka yi masa don ya yi bayani kan zarge-zargin da ‘yan sanda ke masa, kana bai kuma bai wa ‘yan sanda dalilinsa na kin zuwa ba, ya dai ki mutunta musu gayyatar.

“Sanatan ya shiga jerin wadanda rundunar ‘yan sandan Kogi ke nema ruwa a jallo ne kan zargin ta’addanci kokarin kisan kai da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba,” Inji ‘yan sandan.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!