An Sulhuta Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Jihohi A Kan Mallakin Ma’adanai — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

An Sulhuta Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Jihohi A Kan Mallakin Ma’adanai

Published

on


Hukumar ma’adanai da ci gaban albarkantun kasa NCMMRD ta shiga tsakani don yin sulhu akan rikici tsakanin gwamnatin tarayya akan mallakar ma’adanai. Bayanin hakan ya fito daga Price water house Coopers.

A hirar sa da manema labaraia a Abuja a satin da ya wuce a wurin taron da ake ci gaba da gudanarwa na hakara ma’adanai  shugaban sashen ma’adanai da kasuwanci  Mista  Habeeb Jaiyeola ya sanar da cewar akwai bukatar gwamnatin tarayya da data jahohi suyi aiki a karkashin hukumar don kawo karshen rikicin yadda za a samu damar hakrma’adanan.

Acewar sa, PwC tana yin aiki da gwamnatin tarayya akan samar da tsari da samar da kudi ga masana’antar dake kasar nan.

Jaiyeola  ya sanar dacewar a yanzu wajen ma’adanan suna tare da gwamnatin tarayya ne kuma wannan yana daya daga cikin matan da gwamnatin tarayya ta dauka don kawo karshen rikicin.

Ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta samar da sauki wajen bayar da lasisin hakar ma’adanai.

A karshe ya yi nuni da cewar, ba zai zama wata matsala ba wajen kawo karshen rikicin matukar msu ruwa da tsaki a shirye suke don a kawo karshen rikicin kuma babu wata tantama cewar gwamnatocin jihohi sune keda wajajen hakar ma’adanan.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!