Kotu Ta Daure Dan Acaban Da Ya Yi Lalata Da Yara shida — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotu Ta Daure Dan Acaban Da Ya Yi Lalata Da Yara shida

Published

on


Kotun majistare ta garin Minna, jihar Neja ta daure wani dan acaban da aka same shi da laifin yin luwadi da wasu yara su shida, kotun ta daure mutumin mai suna Adamu Muhammad dan shekaru 23, daurin shekaru hudu a gidan yari.

Dan Sanda mai shigar da kara, ASP Daniel Ikwoche ya gabatarwa da kotu bayanin shi, inda yake cewa, wani mutum mai suna Yusuf Buhari ne ya kawo karar Adamu a ranar 6 ga watan Oktoba, a ofishin su da yake Chanchaga, inda yace wanda ake zargin ya lalata da dan shi mai shekaru 10, mai suna Muhammad, a dakin shi dake kauyen Korokpa a Minna.

Sannan kuma an kama shi yana lalata da wasu yaran daban, ‘yan shekaru 10 da shekaru 12, duk dai a dakin shi dake kauyen Korokpa, lokacin da mai shara’a ya karanta mishi abinda ake tuhumarshi da aikatawa, ya amince da laifin shi, ya kuma roki kotu ta mishi sassauci.

Kotun ta yanke wa Adamu hukunci daidai da tanadin shashe na 157 na kundin laifukka, inda zai yi shekaru hudu a gidan yari, tare da aiki mai mugun wahala, sannan babu zabin biyan tara.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!