NIMC Ta Bukaci ‘Yan Jarida Su Wayarwa Da Al’umma Kai Su Yi Katin Dan Kasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

NIMC Ta Bukaci ‘Yan Jarida Su Wayarwa Da Al’umma Kai Su Yi Katin Dan Kasa

Published

on


Darakta janar din hukumar NIMC, mai samar da katin dan kasa, Mista Aliyu Aziz, ya bukaci ‘yan jarida da su yi kokarin wayar ma ‘yan Nijeriya kai, saboda su yi katin dan kasa, ta hanyar rahotanninsu.
Aziz ya yi kiran ne a yayin da jami’an hukumar suka kaiwa Abdul Gombe, manajan-darekta na rukunin kamfanin jaridar Leadership ziyara a ofishin sa dake Abuja.
Aziz ya yi bayanin ayyukan hukumar, inda yace alhakinta ne ta samarwa ‘yan Nijeriya katin shaidar zama dan kasa, da kuma samar wa da bakin da suka shigo kasa bisa ka’ida katin shaida, kuma a cewarshi hukumar tana kokarin yin aikin nata yadda ya dace.
‘Aikin ‘yan jarida ne wayar da kan al’umma, musamman a batutuwa masu muhimmanci irin wadannan, in gwamnati da kamfanoni basu takamamen bayani akan mutum ba, ba bu yadda za ayi a mishi abinda ya dace a lokacin da ya dace, musamman abubuwa da suka shafi tallafin noma, tallafin karatu, fansho, tallafin karatu da ma sauransu.’ Inji Aziz
Aziz ya kara da cewa: Mallakin katin shaidar zama dan kasa, zai baka damar yin mu’amala da kamfanoni da gwamnati yadda ya dace, don haka yakamata ‘yan jarida su yi abinda ya dace wajen ilimantarwa da wayar da kan al’umma, su je su yi katin shaidar zama dan kasa.
Shi ma Abdul Gombe ya tofa albarkacin bakinshi, inda ya ce: lallai ‘yan jaridu suna da rawar takawa, kuma a shirye suke su hada kai da hukumar don wayewar da al’umma kai, saboda muhimmanci yin katin shaidar dan kasan.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!