Badakalar Bidiyon Cin Hanci — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BUDADDIYAR WASIKA

Badakalar Bidiyon Cin Hanci

Published

on


Tsagwaron son kai irin na Kwankwaso, saboda burinsa na tsayawa takara a shekarar 2015, ta sa ya kakaba mana Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan Kano. Ba zan manta ba a ranar da Buhari ya zo kaddamar da takarar gwamna a Kano, ni da abokaina muna kallon taron a talabijin sai na ce musu “Kun ga Kwankwaso da Ganduje, na ba su wata shida kafin a ji kansu” amma akasarinsu ba su yarda da hasashe na ba. Duk da cewa ni ba Dan-duba bane, amma kasancewar sanin da na yi wa Ganduje tun daga 1999, kuma da yadda ya ke biyayya ga Kwankwaso na san cewa likimo kawai ya yi, ya na jiran lokaci. Tarihi dai ya wanke ni bi sa ga wannan hasashe nawa.

A lokacin da Ganduje ya kuduri niyyar mulkar Kano cikin karshen shekarun 1990, lokacin ya na kwamishan ayyuka a lokacin mulkin sojoji, ya kasance mai kwazon aiki kasancewa cikin dare ma ya na yawon duba ayyuka. Wannan shine harsashin da ya kafa na takararsa, domin har mutanen Kano su yi masa lakabi da “Ganduje, gandun aiki”. Ka san shi mutum ne irin Obasanjo, wato idan ka kalli fuskarsu sai ka raina su, ka zata cewa dolaye ne, amma duk wanda ya tsammaci haka ya kan sha mamaki. Bayan ya bar aikin gwamnati tare da kafa wancan suna na “Gandun aiki” sai ya tsunduma a siyasa inda cikin lokaci kankane ya gigita sabuwar jam’yyar PDP. Zan iya cewa Ganduje ne ya lalata siyasar Kano, ba don komai ba sai don cewa duk da cewa su Abubakar Rimi na raye a lokacin, kuma su ke jagorancin siyasa, amma da ya zo ya yi facaka da kudi sai ga shi ya toshe bakin shugabannin PDP tare da siye delegate, kuma ya kama hanyar kada Kwankwaso a takarar fitar da gwani na gwamna. Wannan lamari ya kusa keta jam’iyyar gida biyu amma daga karshe a ka yi masalahar cewa ya janyewa Kwankwaso, sai a bashi mataimaki yadda daga baya zai gaji Kwankwaso.

Wanda duk ya yi mu’amala da Ganduje ya san cewa shi dan jari hujja ne. Ya shigo gidan gwamnati da buri, wanda ya wuce nasa shi kadai har da na iyalinsa. Domin matarsa ta yi kane-kane cikin harkokin mulki yadda komai sai da saninta  a ke yi. Kwamishinoni, ma’aikata, yan siyasa da yan kwangila a kullum na kai caffa wurinta domin kada su sami akasi. Munga yadda a baya Turai Yar’Adua ta yi irin wannan mulki a kasarnan. A bikin ‘yarsu mun ga irin tambelen da a ka yi wadda ya tabbatar da cewa duk inda ka ga irin wannan rashin da’a ka san cewa hakika namijin gidan ba shi ke da cikakken iko ba, sai dai idan mijin-ta-ce ne, wanda gwamnan da kansa ya amsa hakan yayin da ya ke maidawa Kwankwaso martini sanda ya soki bikin.

Manufar Ganduje ta jari hujja ta sa ya na ganin cewa idan ya buya a bayan Buhari, sannan ya jawo manya ‘yan jari hujja jikinsa tare da kyautata musu, ya ishe shi wajen zama a kan mulki kuma ya zarce a karo na biyu, saboda ya manta cewa mulki na Allah ne. Da ka kalli irin mutanen da ya kewaye kansa da su a cikin gwamnatinsa tun hawansa, kasan cewa ba za’a yi abin kirki ba. Kuma duk cikinsu ba mai iya fitowa karara ya bashi shawara ta gaskiya, sannan a gida kuma sai dai a kara masa kaimi.

Saura kiris Sarkinmu mai surutu ya rasa kujerarsa, yayin da ya raina Gwamna a cikin taro da ya yi kokarin sukar shirin sa na aikin jirgin kasa a birnin Kano wanda zai lakume sama da dala biliyan daya (idan ka lissafa kaso 15-25% da ake karba daga yan kwangila ka san kudaden gaske ne). Gwamnan ya sa hukumar cin hanci da rashawa ta Kano ta fara bincikar masaurata. Sai da gungun manya a fadin Arewacin kasar nan su ka yi ta kai ruwa rana sannan da kyar aka lallashe shi ya janye kudurinsa na cire Sarkin, kuma ba kunya ba tsoro ya janye binciken masarautar.

Lokacin da jam’iyyar APC ta bawa jihohi zabin yin zabukan fitar da gwani na jam’iyya a tsarin wakilai ko kato-bayan-kato, saboda munafinci sai Kano ta zabi yin kato-bayan-kato wanda ya baiwa masu zabe da ‘yan takara kwarin gwiwa, ashe shi gwamna ya shirya yin kakabe ne kawai. Yawancin yan takarkaru sun yi korafin cewa ba’a basu dama kowacce iri ba, sai dai tursasa su don janyewa wasu.

Siyasar Kano ba ta taba samun kanta cikin mawuyacin hali na gaba-sayaki-baya-damisa, irin na wannan lokaci ba, domin ba wani dan takarar gwamna a APC ko PDP da zai sa ka ji kwarin gwiwa. Don Karin bacin rai, sai Ganduje ya jajibo shekarau cikin APC ya kuma kakaba wa mazabar sanatan tsakiya ta Kano. Don Allah yaushe kanawa za su farka daga barci ne? mu duba yadda Lagos tun 1999 sai gaba-gaba su ke yi yadda a yanzu za su iya zama da kafafuwansu ba tare da gwamnatin tarayya ba. Ku duba yadda Tinubu ya kori Ambode saboda kaucewa tsarin ci gaba na shekaru 25 da su ka fara. Amma mu a Kano ba wani tsari, duk da cewa shekaru 70 a baya Kano ta fara irin wannan tsari, amma kullum sai baya mu ke yi. Ina malamai, yan boko, sarakai, yan siyasa da attajiran Kano, haka zamu ci gaba da zama kara zube? Mulki shine abinda ya fi komai mahimmanci a al’umma, amma sai muke masa rikon sakainar kasha, mu rika barin kowanne kare da doki ya mulke mu? Mu sani cewa idan mu ka ci gaba a haka wallahi ‘yan baya sai sun tsine mana.

A baya-bayan nan mun ga yadda dan majalisa mafi kima da tagomashi a kasar nan, dan asalin jihar Kano, wato Faruk Lawan, shugaban Integrity group a majalisar tarayya wadda ta kasance kungiyar ‘yan majalisa da ke sawa da hanawa a kasar nan. A lokacin ya na ganiyar daukakarsa tare da karfin fada a ji, sai ga shi an  kama shi yana karbar cin hanci na daloli yana sakawa cikin hularsa. An nadi wannan lamari a faifan bidiyo yadda duniya ta gani. Kwatsam kuma sai gashi a wanann satin an saki faya-fayen bidiyo inda Gwamnan Kano ke karbar kudade na cin hanci.

Wannan abin kunya ya isa, amma sai gashi kwamishinansa na yada labarai ya saki wani bayani wanda a ciki, maimakon ya bada hujja da za ta wanke maigidan nasa sai ya bige da cewa ina wanda ya bada cin hancin, domin doka ta hana bayarwa da karbar rashawa. Wannan bayani ba abinda ya yi sai tabbatar da zargin, domin ya yi kokarin jefa laifin ga mai bayarwa. Ko shari’a ta na iya uzuri ga wanda aka tursasa ya bayar da cin hanci idan babu yadda zai yi. Kuma wannan faifai na bidiyo zai karfafa jita-jita da ke cewa matar gwamnan ma na karbar irin wannan toshiyar baki tunda ga mijinta ya karba. Duk wanda ya kalli wadannan bidiyo, a mabanbanta lokutai da yanayin shigar da gwamnan ya yi da zantuttuka da ke ciki, zai sami gamsuwa. Akwa sunan kamfuna da aka ambata sun bayar da cin hancin har da ma inda aka ce wani kamfani ya ki bayarwa, sakamakon da ya sa aka daina bashi aiki.

Kira na ga Gwamna a wannan gaba shine, ya kamata ya ajiye aiki a kashin kansa kafin tonon sililin ya yi nisa, ya baiwa mataimakinsa Nasiru Gawuna, damar ya maye gurbinsa a takarar gwamna, ina ganin hakan zai fiye masa sauki da ma al’ummar jihar Kano. Idan gwamna ya ki wannan shawara ina ganin babu abinda ya rage wa APC da Baba Buhari illa su saka majalisar Kano ta yi bincike a bainar jama’a, sannan ta yi adalci, idan gwamna na da laifi sai su tsige shi kamar yadda doka ta tanada.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!