Kungiyar Marubuta Wakokin Hausa Ta Yi Taronta Na Farko A Zaria — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Kungiyar Marubuta Wakokin Hausa Ta Yi Taronta Na Farko A Zaria

Published

on


A watan Maris din wannan shekara ne ta Dubu Biyu Da Sha Takwas ne da ya gabata aka kyankyashe sabuwar kungiyar marubuta wakokin Hausa da manazarta a karkashin jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi, kungiyar da aka rada mata suna da Gamayyar Marubuta Da Manazarta Wakokin Hausa kuma aka yi mata take da ‘Hikima Jari Ce’. Sannan aka nada Malam Sulaiman Salisu Maibazazzagiya a matsayin shugaban kungiyar na riko a mataki na kasa baki daya. An yi amfani da babban taron marubutan Hausa na duniya ne da aka yi a birnin Dikko cikin watan Maris din wannan shekara ta 2018 wajen dabbaka wannan kungiya ta fasihan marubuta wakokin Hausa.

Taron kungiyar marubuta wakokin dai da aka yi ranar Lahadi 7-10-2018 a tsangayar nazarin harsunan Najeriya na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, shi ne na farko da aka yi tun bayan kyankyashe kungiyar, duk da dai a matakin jahohi wasu sun yi taruka fiye ma da sau daya musamman ma kungiyar ta jahar Kano da Malam Ibrahim Hamisu yake jagoranta.

Taron marubuta wakokin na kasa da aka yi da nufin farfado da rubutacciyar waka ya samu tagomashin halartar manyan marubuta wakokin Hausa daga jahohin daban-daban na arewacin Najeriya da suka hada da: Kaduna, Kano, Bauchi, Kebbi, Katsina, Zamfara, Abuja da kuma Yobe.

Baya ga dandazon mawakan da suka samu halarta, taron kuma ya samu sanya a albarkar manyan malaman adabi da suka hada da: Farfesa Magaji Tsoho Yakadawa wanda shi ne ya jagoranci taron kuma daya daga cikin iyayen kungiyar, da Malam Sulaiman Maibazazzagiya wato shugaban kungiyar na kasa, sannan akwai Dr. Hauwa Bugaje, Dr. Habibu Ibrahim Kankara, Dr. Abubakar Sarki, Dr. Adamu Abdussalam, Dr. Adamu Kubau, Ustaz Abdurrahman Maluman Matazu, Ustaz Mahmud Misau, Malam Ibrahim Garba Nayaya da dai sauransu.

A jawabinsa shugaban kungiyar ya ba da takaitaccen tarihin kafuwar kungiyar da kuma fayyace manufofinta da kuma kudirorin da ta sanya a gaba, ciki ya ambaci tsakace rubutattun wakokin Hausa saboda gudun salwancesarsu, sanya gasar wakokin Hausa don kara zaburarwa da kuma samar da sabbin wakoki, sannan sadar da zumunci da kuma taimakon juna.

Mawaka dai da yawa sun baje kolin fasaharsu a wajen wannan babban taro da suka hada da: Dalhat Suraj Maisharifiya da wakarsa mai taken (Mutuwa), Maluman Matazu (Muhimmancin Takalmi), Dr. Adamu Abdussalam (Sakar Hausa), Ustaz Mahmud Misau (Rayuwar Zamani), Ibrahim Hamisu (Cima Ta Kirki), Mukhtar Mudi Spikin (Hira Da Tsuntsu), Musa Sulaiman Koko (Rikon Amana), Habibu Nijjar Bello (Duniya), Rukayya M Bello (Malam), Adamu Magaji (Shaye-shaye), Usman Abubakar Maikifi (Rukunan Imani), Malam. Sulaiman Maibazazzagiya (Tuna Baya).

Malama Dr. Hauwa Bugaje daya daga cikin malaman da suka samu halartar taron, a cikin jawabinta ta nuna matukar farin ciki da jin dadinta saboda jin ashe har yanzu akwai fasihan mawakan Hausa na asali da aka sani ba wai masu kida da juyi ba, sai dai kuma ta koka kan halin da nazarin wakokin Hausa ke ciki a yau a cikin jami’o’i da cewa, “Mun dade shekara da shekaru ana nazarin wakokin Hausa irin na su Shehu Usman Bin Fodio, aka gangaro karni na Ashirin na su Mudi Spikin, Sa’adu Zungur, Akilu Aliyu. Hasalima ina ga yara sun gaji da nazarinsu ne shi ya sa ba su sha’awarp daukar wakokin. Saboda tun kana aji Daya in ka shigo su za a ta yi maka har ka je aji Hudu. Ka gama ka zo mastas su ne, kullum mutum yana abu Daya. To dan adam yana son sabon abu. Kuma kowacce al’umma adabinta yana wakiltar zamaninta ne, to mun fahimci jiya kuma muna so mu ga yau ta mahangar wakokinku, shin ya za ku fito mana da yau, yadda idan nan da shekaru Dari al’ummar zamani mai zuwa za su kalle mu ta mahangar wakokinku, su dauki wakokin su nazari su fahimci ya muka rayu, wadanne matsaloli muka fuskanta kamar yadda su Shehu Usmanu suka suka fuskanci matsalar sarakuna da kuma malaman bidi’a na wancan zamani.”

Malama Hauwa Bugaje ta ci gaba da cewa, “Sannan kirana gare ku shi ne a yi kokari a killace wakokin a rubuce kada su kasance a kan yana ko kafar sadarwa ta zamani irin su whatsapp ko facebook, saboda wadannan abubuwa ne da nan da nan zamani zai iya kawar da su. Kullum sabbin abubuwa ne suke fitowa. Don haka a yi kokari a samu yadda za a taskace su a rubuce, yadda mu jami’o’i za mu kokarin ganin cewa an mun sa su a manhajar koyarwa an fara nazarinsu, sannan kuma gaba a fadada bincike.

Domin yanzu kusan sai dalibi ya g in y dauki topic na rubutacciyar waka sai ya ga ai karyar ta kare, su Farfesa Dangambo, Farfesa Dalhatu Muhammad, Farfesa Yakadawa kamar sun cinye komai, in ka zo sai ka rasa me za ka nazarta. Don da ka dauko wakokin Aliyu Namangi a ce an yi PhD a kai Birniwa ya yi Yakadawa ma ya yi, ko Akilu Aliyu a ce Farfesa Dalhatu Muhammad ya yi, in kuma ka dauko wakokin masu jahadi a ce ma Farfesa Dangambo. Duk ta inda ka billo kuma haka ne.

Ni kaina lokacin da nake mastas sai da nai ta walagigi sannan a karshe na ce bari na kama rubutattun mata na karni na Ashirin Da Daya, kuma su din ma na ga ai an yi ayyuka a kan su Hassana Sufi, Hauwa Gwaram.

Sai na ga to ya zan yi na samarwa da kaina mafita, sai na dauki wadanda ba a yi aiki a kansu ba wato su Amina Anda, Rayhanatu Usman da dai sauransu. To a gaskiyar lamari duniyar ilimi tana bukatar rubutacciyar waka a kodayaushe, ana kuma kishirwarta.”

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!