Bayan Ficewa Daga APC, Shehu Sani Ya Yi Fashin Baki Kan Takara A 2019 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Bayan Ficewa Daga APC, Shehu Sani Ya Yi Fashin Baki Kan Takara A 2019

Published

on


Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani, ya bayyana cewa zai yi takara a babban zaben nan da ke tafe na 2019 duk da cewa ya fice daga Jam’iyyar APC.

A ranar Asabar ne Shehu Sani, ya bayyana ficewar na shi daga cikin Jam’iyyar ta APC, bayan da Jam’iyyar ta mika sunan Uba Sani, wanda na hannun daman Gwamnan Jihar ne, Nasir El-Rufai, a matsayin wanda zai tsaya mata takara a mazabar na shi.

Cikin sanrawar da ya lika a shafin sa na Facebook a ranar Lahadi da safe Shehu Sani ya ce, “Ina mika godiya ga daukacin magoya bayana da abokanan arziki a kan goyon bayan da suka nu na mani a bisa shawarata ta ficewa daga Jam’iyyar APC.

“Ina son na tabbatar maku da cewa, nan da kwanaki biyu zan sanar da ku sabuwar Jam’iyyar da na koma. Ku kuma kwana da tabbacin zan tsaya takara a wannan babban zaben da ke tafe Insha Allah.”

Kawo yanzun dai babu tabbacin ko wace Jam’iyya ce Shehu Sani, zai koma, kuma a wane mukami ne yake da nufin tsayawa takarar.

A bisa tsarin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa dai a kan yanda ta tsara zabukan na 2019, za ta kulle karban sunayen ‘yan takara ne da bayanan su kansu ‘yan takaran a ranar 18 ga watan Oktoba, ga masu neman tsayawa takarar shugabancin kasa da kuma majalisun tarayya.

Amma Jam’iyyu suna da daman mika sunayen ‘yan takaran su na gwamnoni da majalisun Jihohi har zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba.

Sannan kuma Jam’iyyun suna da daman canza ‘yan takaran na su na shugabancin kasa da majalisun tarayya har zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba, suna kuma da daman yin hakan har zuwa ranar 1 ga watan Disamba ga masu neman mukaman gwamna da na majalisun Jihohi.

A ranar Asabar ce Shehu Sani, ya sanar da ficewar na shi daga cikin Jam’iyyar a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban Jam’iyyar na mazaba ta 6 da ke Tudun wada Kaduna.

A cikin wasikar yana cewa, “Ina farin cikin sanar da kai ficewa ta daga cikin Jam’iyyar APC.”

“Na shiga cikin Jam’iyyar APC ne na kuma zauna a cikin ta duk rintsi a bisa tabbacin da nake da shi na kasancewarta Jam’iyyar da ke kokarin tabbatar da tsarin dimokuradiyya wanda nake da matukar kishin hakan, sai dai me, nan gaba ne zai tabbata kan ko wace irin dimokuradiyya ce Jam’iyyar ta APC ke kokarin tabbatarwa.

“A lokacin da nake ficewa daga Jam’iyyar ta APC a wannan lokacin, ina son na gode wa Jam’iyyar da ta ba ni daman yin aiki a matsayin Sanata a majalisar dattijai ta Nijeriya.

“Ina ma Jam’iyyar fatan alheri a nan gaba, ina kuma rokon ka da ka karbi wannan ficewa da na yi daga cikin Jam’iyyar a bisa radin kaina.

An dai yi ta samun cece-kuce a kan shawarar da Jam’iyyar ta yanke na baiwa wasu Sanatoci tikitin kai tsaye.

Kwanaki kadan da Jam’iyyar ta APC ta bayyana Shehu Sani, a matsayin dan takaranta daya tilo da ta wanke domin tsayawa takara a mazabar ta Kaduna ta tsakiya, sai gwamnatin Jihar Kaduna da jami’anta suka kalubalanci shawarar da uwar Jam’iyyar ta kasa ta zartar, wanda hakan ya tilasta wa uwar Jam’iyyar canza shawarar da ta rigaya ta yanke a baya.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!