Buhari Zai Sake Lashe Zaben 2019 –Nda-Isaiah — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Buhari Zai Sake Lashe Zaben 2019 –Nda-Isaiah

Published

on


Shugaban rukunin kamfanonin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, ya bayyana tabbacin da yake da shi na cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, zai sake lashe takarar shugabancin kasar nan a babban zaben 2019.

Sam Nda-Isaiah ya ce, kyawawan ayyukan da shugaban ya yi a karkashin gwamnatin Jam’iyyar APC ne za su sake maido da shi a karagar mulkin kasar nan.

Sam Nda-Isaiah, ya yi wannan bayanin ne ga manema labarai a Akure, ta Jihar Ondo, jim kadan da nada shi Sarautar, ‘Aare Baroyin’ na dadaddar masautar ta Akure, a karshen makon nan.

“Ni dan Jam’iyyar APC ne, zan ci gaba da goyon bayan dan takaranmu na shugabancin kasa, Muhammadu Buhari, a wannan babban zaben na 2019.

“Tabbas zai cinye zaben, duk da yake ba za mu yi sakaci da lamurran ba, amma dai muna da tabbacin zai lashe zaben ba tare da wani wahala ba.

A cewar sa, kasar nan ta samu canji mai yawa a karkashin gwamnatin ta Jam’iyyar APC, musamman a fannin noma.

“Abubuwa sun fara farfadowa, kasarmu ta zama ma fi girman tattalin arziki a Afrika duk da irin kalubalen da muka yi ta fuskanta.

“Kar ku manta da irin halin ni-‘ya-sun da tattalin arzikinmu ya shiga, don haka tilas ne abubuwa su canza, yanzun kuma mun fita daga wannan yanayin na tabarbarewar tattalin arzikin.

“Kwanan nan, za ku ga kasar nan ta zama mai dogaro da kanta ta fuskacin shinkafar da za mu ci, wanda hakan bai taba faruwa ba a baya.

“Ba cewa nake yi mun iya cika duk alkawurran da muka yi ba, amma dai kun san ai muna kan hanyar hakan.

“Kowa ya ganin ma idonsa, ai dan adam tara yake bai cika goma ba, ina da tabbacin za mu sake lashe zaben.”

Da yake magana a kan zabukan fitar da gwani na Jam’iyyar wadanda suka janyo cece-kuce masu yawa a tsakanin ‘ya’yan Jam’iyyar, Nda-Isaiah, ya bayar da tabbacin duk za a sasanta komai kafin babban zaben na 2019.

“Ban ji dadi ba, musamman a kan abin da ya faru a Jihar Zamfara, duk da yake dai mun je kotu, amma dai ban san yanda lamarin zai karke ne ba.

“In har muna son ci gaba da mulkin kasar nan, ya zama tilas mu bayar da misalin abin da ya fi kyau a bisa na Jam’iyyar PDP.

“Za dai mu yi nasara, amma dai gaskiya an yi abin da bai kamata a ce ya faru a hakan ba a wajen.”

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!