Kwastan Na Ci Gaba Da Farautar Wadanda Suka Shigo Da Miya Daga Chana — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kwastan Na Ci Gaba Da Farautar Wadanda Suka Shigo Da Miya Daga Chana

Published

on


Bayan cafke tukunyoyin miyar da aka shigo da su daga kasar Chana da jami’an hukumar kwamtan ta yi, bayanai na nuna cewa, har yanzu wanda ya jigilar shigo da miyar ya ranta ana kare ana kuma nemansa ruwa a jallo.

Da yak e bayanni ga ,mane ma labarai, jami’in watsa labarai na rundunar ‘Strike Force’ Mista I. K. Angulu, ya bayyana cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano inda aka nufa da kwantaina miyar da kuma sauran kayayykin da ke, duk da cewa harb yanzu ana ci gaba da neman wanda ya yi jigilar shigo da kayyakin daga daya.

Ya kuma ci gaba da cewa, “ana ci gaba da gudabar da bincikena kan miyar da aka shigo dasu  da sauran abincin dake a cikin kwantainan. Har yanzu bamu kama wanda ya shigo da kayyakin ba. mun dai kama direban motar kuma yana bamu bayanai ,masu mahimanci na abon day a shafi inda a aka shirya kai kayayakin da kuma bayanan wanada ya shigo da kayyakin da kuma inda aka shiya kai kayyakin, zamu sanar da jama’a da zaran mun kammala binciken namu gaba daya.”

Idan za a iy tunawa hukumar Kwastam NCS sun cafke tukunyoyin miya da sauran abinci da aka shi go das u daga kaar Chana na kudi fiye da Naira27,960,000.

An bayar da izinin fita da kayan daga wani tashar jirgi a garin Legas, a kan hanya ne rundunar hukumar kwastama na ‘Strike Force’ suka cafke su bayan da aka samu bayanai na sirri  akan abin da suke dauke da shi.

Da yak e jawabi ga ‘yan jarida a Legas tare kuma da gabatr wad a jama’a kayyakun da aka cafke, a tsakanin ranar 19 ga watan Satumba da kuma ranar 18 na Oktoba 2018, maytaimakin shugaban hukumar Kwastam na rudunar ‘CGC Strike Force’, Abdullahi Kirawa, y ace, wanna lamarin abin kunya ne kuma da wulakanci, “har abin ya kai ana shigoka da miya cikin kasar nan.”

Ya kuma yi korafin abubuwan da aka shigo da su ba za a iya tantance ko dame dame ba ne don kuwa da yaren Chana aka yi dukkan rubutun da aka yi a kan kwamtainan, abubuwan kuma na iya zama baraza ga al’ummar kasar na gabi daya.

lallai wanan abun kunya ne ga kasar nan kuma abin kunya ne.

“Dole mu rage tsanananin bukatarmu na abinci kasashen waje mu rungumi abincimu na gida mu kuma guje wa fada wa irin wannan sana’a gaba daya,don kuwa wasu daga cikin abincin da aka shigo dasu sun fara rubewa abin da kuma zai iya cutar da wadanda za su yi amfani dasu.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!