Real Madrid Ta Canja Shawara Kan Dan Wasa Bincius — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Canja Shawara Kan Dan Wasa Bincius

Published

on


Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wato Florentine Perez ya ga uwar bari, a inda ya ce zai dawo da dan wasa Bincius JR cikin babbar kungiyar ta Real Madrid ko zai taimakawa kungiyar ta fita daga halin da take ciki.

Mahukuntan kungiyar kafin a fara gasar Laliga da gasar zakarun turai sun yanke shawarar barin wannan matashin dan wasa a karamar kungiyar ta Real Madrid domin ya sake gogewa kafin ya shiga babbar tawaga.

Duba da cewa akwai gudun mawar da dan wasan zai bayar shine shugaban ya ce za a dawo dashi babbar kungiyar domin daman yana buga wasa a babbar kungiya lokacin da yana kasar Brazil yana buga wasa.

Real Madrid dai tana cikin wani hali na rashin samun nasara a wasanni bayan da kungiyar ta buga wasanni biyar ba tare data samu nasara ba ciki hard a wasan da kungiyar tasha kashi a ranar Asabar a hannun Lebente.

A mako mai zuwa ne kuma Barcelona za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a filin wasa na Nou Camp wasan da dan wasa Messi ba zai buga ba saboda ya ji ciwo a wasan daya buga a ranar Asabar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!