2019: Ba A Nan Gizo Ya Ke Sakar Ba..! — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

2019: Ba A Nan Gizo Ya Ke Sakar Ba..!

Published

on


Sau da yawa masu rike da madafun iko su kan mance da abinda ka iya faruwa a can gaba lokacin da idanunsu ya rufe su ke son tabbatar da nasu ko son ransu a lokacin zaben fitar da gwani na jam’iyyunsu.

A fili ta ke cewa, tun daga 1999 lokacin da a ka mayar da mulki ga hannun farar hula a Najeriya zuwa yanzu wadanda shugaban kasa ko na hannun damansa ko gwamnoni ko na hannun damansu ko shugabannin uwar jam’iyya ta kasa ko na jihohi su ke da muradin tsayarwa takara a ka zo gudanar da zaben fitar da gwanayen jam’iyya, idanunsu ya kan rufe su kasa hangen abinda ka iya faruwa matukar an tsayar da wanda jama’a ba su so ko kuma wanda a ke iya gane cewa bai cancanta ba.

Wannan matsalar ba wai ta tsaya a kan jam’iyyar da ke mulki a kasa ba ne kadai, a’a, matsala ce wacce ta ke mamaye dukkan manyan jam’iyyun kasar, wato har na adawa, musamman ma babbar jam’iyyar a adawa a kasar, kamar ANPP, CAN ko CPC a baya ko kuma PDP a yanzu kenan. Jiga-jigan jam’iyyun su ka n bankara ta karfi da yaji su tsayar da nasu a jam’iyyar da su ke da iko da ita ko su ke fada a ji a cikinta.

Amma babban abinda ba sa hange a irin wannan runtsin shi ne lokacin da za a gudanar da babban zabe na gama-gari, wanda shi ne a ke iya gane cewa wancan bankarawar da su ka yi ba ta yi amfanin komai ba, domin jam’iyyu da dama a lokutan daban-daban sun sha faduwa su rasa mulkinsu sakamakon tsayar da dan takarar da bai zai iya kawo kujerar ba a lokacin babban zabe na gama-garin.

Irin wannan abin na mantuwa da rashin hangen nesa shi ne mu ka gani a kwana-kwanan lokacin gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyun kasar nan, wadanda a ka kammala. A bayyane ta ke cewa, ba wai kawai mutanen gari masu kada kuri’a a zaben gama-gari ba, a’a, hatta su kansu ’ya’yan jam’iyyun ba su jin dadin yadda a ka bankara su wajen tsayar mu su da ’yan takara ba. To, ina ga mutanen gari, wadanda ba su da kishin wata jam’iyya guda, illa dai kishin wanda zai iya kawo mu su cigaba? Shin ta kaka a irin hakan wannan dan takara zai iya kai labari tunda ’yan jam’iyyar ma ba su tare da shi?

Hakika wannan ba karamar cutarwa ba ce ga mabiya jam’iyyar, wadanda yawancinsu su ma talakawa ne masu kishin jam’iyyar tasu da ganin cewa ta kai ga gaci, to amma son rai na jagororinta ya sanya mu su bakin cikin faduwa a zabe tare da kallon abokan adawarsu su na murnar cin zabe.

To, ba wai faduwa a zabe ne kadai ya ke kawo illa a tsayar da dan takarar da bai cancanta ba; wata illar da ta ke biyo bayan hakan ita ce, shirya yadda za a tafka magudi ko ta halin kaka. Wanna ya na faruwa ne saboda su da su ka tsaya takarar da wadanda su ka tsayar da su sun san cewa mutane ba za su zabe su ba. Don haka tilas su bi kowacce irin hanya ko da kuwa haramtacciya ce wajen ganin sun dare kujerar. Ka ga kenan rashin tsayar da dan takarar da ya cancanta ya haifar da tafka magudin zabe, domi  idan ba hakan su ka yi ba, babu yadda za a yi su lashe zaben. Su kansu sun san hakan kuma da ma tun asali hakan su ke shiryawa, shi ya sa su ke dagewa a kan sai sun tsayar da nasu ko ta halin kaka ne!

Duk ba a nan gizo ya ke sakar ba; babbar masifar da ta ke samun ’yan Najeriya sakamakon rashin tsayar da ’yan takarar da ba su cancanta ba ita ce, ba su iya aiwatar da ayyukan da a ka dora su, domin su. Wannan rashin dacewa da rashin cancanta su ne su ke bibiya da biyo bayan zaben da a ka gudanar, wanda bayan a mafi yawan lokuta a ke shafe shekaru hudu a na mulki ba tare da tsinana wa wadanda a ke mulki abin a zo a gani ba.

Da a ce jiga-jigan jam’iyya za su daina yin kama-karya su na nada wadanda za su biya mu su bukatunsu na kashin kansu, su goyi da bayan mutane nagari wadanda su ka cancanci rike mukaman da a ke gudanar da zabuka a kansu, hakika da Najeriya da ’yan Najeriya tabbas sun fita daga matsalar su ke cik

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!