Kar A Maimaita Kuskuren Zaben PDP A 2019  –Balarabe Musa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kar A Maimaita Kuskuren Zaben PDP A 2019  –Balarabe Musa

Published

on


Tsohon gwamna tsohuwar jihar, Alhaji Balarabe Musa, ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su kuskura su yi kasadar sake zaban jam’iyyar PDP a zaben 2019 dake tafe.

Alhaji Balarabe Musa ya yi wanna bayanin ne daga Kaduna a tattawarsa ta wayar salula tare da wani dan jarida NAN, ya ce al’amurra za su yi matukar lallacewa in har aka yarda jam’iyyar adawa ta PDP ta sake dawo wa karagar mulki a kasar nan.

Ya ce, jami’yyar PDP ta yi mulkin kasar nan na tsawon shekara 16 kafin zuwan wannna gwamnatiun a shekarar 2015, “Babu abin da suka kawo a kasar nan sai talauci da rashin ci gaba.”

Ya kuma kara da cewa, jam’iyyar PDP ta kusan dukusar da kasar nan gaba daya ta hanyar cin hanci da allubazaranci da kudaden jama’a a yayin da suke a kan karagar mulki.

Tsoho gwamnan ya ce, duk da cewa, al’amurra ba su gyaru yadda ya kamata ba a karkashin wannna gwamnatin na APC, bai kamata ‘yan Nijeriya su kara kasadan tunanin cewa, jam’iyyar PDP za ta gyara wani abu a kasar nan.

Daga nan ya kuma ce, jami’iyyar PDP ba ta da mutumcin sake dawo wa karagar mulki, a kan haka ya bukaci a sake nemo wasu masu mutumcin da za a damka wa mulkin kasar nan wadanda za su kawo gagarumin canji da ake bukata.”

“Ban dalilin da PDP za ta sake neman sake dawo wa karagar mulki ba, ban fahinci dalilinsu ba, su dawo su yi me? Jam’iyyar ne ta haifar da dukkan matsalolin da ake fuskanta a tsawon shekara 16 da suka yi suna mulki, wannan ba zai yiwu ba!

“Lallai abubuwa ba sa tafiyar daidai a kasar nan a halin yanzu amman ina tsammanin larumurra za su kara lallacewa ne in har PDP ta sake dawo wa karagar mulki.

“Bai kamata ‘yan Nijeriya su amince da jam’iyyar PDP ba, abin da muke bukata a halin yanzu shi ne wasu yan siyasa na daban wadanda za su samar wa da kasar nan mulki na gari da jama’a ke bukata.” he said.

Daga nan ya kiuma ce, a ‘yan shekarun nan kudi ya yi tasiri a siyasar kasar nan abin da ya yi sanadiyyar fitowar ‘yan siyasa da ba su da farin jini a wajen jama’a

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!