Rikcin APC: Gwamna Amosun Ya Dirar Wa Oshiomhole — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Rikcin APC: Gwamna Amosun Ya Dirar Wa Oshiomhole

Published

on


Gwanan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya ci gaba da yin watsi da sakamakon zaben fidda gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar, ya kuma zargi shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da hada baki da wasu jigajigan jam’iyar daga Legas inda suka fitar da sakamakon zabe na bogi wadda suka ce Dapo Abiodun ne dan takarar gwamna daga jihar a zaben 2019.

Mista Amosun ya yi wannn a korafin ne a tataunawarsa da ‘yan jarida bayan da ya ranstar da babban jojin jihar, Mosunmola Dipeolu, a ofishinsa dake garin Abeokuta, babban birnin jihar.

Ya yi zargin hanun tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu da kuma tsonhon gwamnan jihar Ogun Segun Osoba a badakalar, yana mai cewa, shirun da suka akan lamarin ya nuna cewa lallai a kwai hannun su a kan lamarin.

“Shugaban kasa ya san ba a yi zabe a jihar Ogun State. Ya cewa, sun tafi Legas ne suka rubuta sakamakon zaben kawai abin da suka yi lallai bai dace ba, in har wani sugaban jam’iyya nan ya ce an yi zaben fidda gwani a jihar Ogun to lallai karya yake yi, ni ne na fadi haka,” inji Mista Amosun.

Gwamnan mai barin gado, bai boye bacin ransa ba, kan rashin halastaccen zaben fidda gwani da jagorancin jam’iyyar ta gudabar ya fitar da Adekunle Akinlade a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar.

“Shugaban kasa ya san babu wani zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar Ogun sai wanda muka gudanar,” inji gwamnan

“Muna zargin Cif Osoba da Bola Tinubu, kuma shiru da suka yi yana nana lallai a kwai hannu su a kan wannn lamari, ku je ku buga bayyanin da na yi ajaridu bana shakkan komai, don gaskiya nake fadi’

“Ba mu ji komai daga bangarensu ba, an yi zabe a jihar Ogun eh ko aa, su fito fili su yi magana sun kasa, su fito su bayyan wa duniya ko anyi zabe ko ba a yi ba, mu dai muna da tabbacin ba a yi zabe ba, sun kuma kasa fitowa su bayyana wa duniya matsayarsu.

“Ranar da suka ce bamu yi zabe ba,za mu fito da dukkan shaidar da muke da shi don duniya ta ganin, sun fitar da sunayen mutane kamar su Leke Adewolu da Mikail Kazeem dukkan

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!