Mukaman Da Buhari Ya Ba ’Yan Jihar Bauchi Bai Amfanar Da Jihar Ba -Ghani — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Mukaman Da Buhari Ya Ba ’Yan Jihar Bauchi Bai Amfanar Da Jihar Ba -Ghani

Published

on


HAMIDU SA’IDU GHANI tsohon shugaban karamar hukumar Bauchi ne tun farkon fara fara mulkin demoradiyya, kana gogaggen dan siyasa ne da suka buga a jiya da yau. A hirarsa da LEADERSHIP Ayau, ya bayyana cewar shugaban kasa Buhari ya yi kokarin baiwa ‘yan jihar Bauchi mukamai daban-daban a gwamnatin tarayya, amma mukaman sun gaza yin amfani wa jama’an jihar ta fuskacin taimakonsu, kana ya tabo batun zaben fitar da gwani na APC, har ma yake cewa da iyuwar APC ta rasa tulin kujeru a sakamakon rashin adal

Ka gabatar wa masu karatunmu da kanka?
Sunana Hamidu Sa’idu Ghani, tsohon zababben shugaban karamar hukumar Bauchi a alif 1999.

Kana da abin cewa dangane da hidimar siyasa a jihar Bauchi da kasa kawo yanzu da muke tsumayar babban zaben 2019?
Eh ba zan rasa abin cewa ba, kasantuwar mutum dan siyasa. Hidimarmu ta Bauchi, a gaskiya ababen da suka wakana a cikin jam’iyyar APC muddin ba hattara aka yi ba to za mu iya rasa kujeru da yawan gaske a sakamakon rashin adalci da aka yi a lokacin zaben fitar da gwani na jam’iyyar; bayan rasa kujerun ma za a iya fadi kasa warwas na rashin samun mulki a jihar. kai tsaye zaben fitar da gwani a APC ba a yi su yadda ya kamata ba, jama’a suna korafe-korafe sosai a kan yadda aka yi zabukan. Musamman a jiharmu ta Bauchi, lallai an samu korafi sosai kan zaben fitar da gwani a APC, wanda hakan barazanace ga zaben 2019 domin za mu iya rasa kujeru ko ma jam’iyyar ta fadi gaba daya kamar yadda na fada maka tun a farko.

Wai shin mene ne ake korafin nan a kansa takamaimai?
Korafi, an ce an yi zaben shugaban jam’iyya, tun a wannan lokacin aka yi son rai aka yi yadda wasu suke so ba yadda mambobin jam’iyya suke so ba, wannan ya wuce. Aka zo kan zaben fitar da gwanaye na jam’iyya aka yi ta kai kawo kan yin amfani da wakilan jam’iyya ‘delegates’ wajen fitar da ‘yan takara daga karshe dai aka tsaida matsaya kan yin kato-bayan-kato, a sakamakon sanin halayen delegates din da kuma sanin halin yadda gwamnan jihar, hakan ya sanya wasu suka yi firgicin sahihancin zaben da za a yi muddin aka yi amfani da delegates, sai kuma gashi an zo an tafka rashin daidai fiye ma da yadda aka tsammata daga wajen delegates, wannan rashin adalcin ne ma ya sanya wasu da dama suke ta ficewa daga cikin jam’iyyar kamar ‘yan majalisunmu, ‘yan takarar gwamnanmu hakan ne ya sanya wasu ma suka gaza shiga takaran a sakamakon rashin gamsuwa na adalci daga karshe dai wannan zaben ‘yar tinke da aka yi a jihar Bauchi sai da jama’a suka gwammace daman an yi amfani ne da delegates din da ya fi.

Wadannan irin korafe-korafen da suke akwai, shin kana ganin idan APC ba ta iya magancesu ba har zuwan 2019 da iyuwar ta gaza samun nasara ko ya kake kallon makomar jam’iyyar dai?
Makomar jam’iyya kamar yadda na fara fada gaskiya APC za ta rasa kujeru da yawan gaske, za kuma ta wargaje din, domin wasu za su fita, yanzu din ma ka ga yadda al’amura suke, wasu fitattu din ma sun yanke cewar sun fita daga jam’iyyar, amma wasu dai basu sanar a bayyana ne bane kawai, wasu kuma sun fita din. Wasu kuma da za su zauna a cikin jam’iyyar na dole su ba za su fita ba suna dai cikinta za su iya yin zagon kasa wa jam’iyyar har ta kai ga rasa samun nasarar da take honkoro.

Idan har ‘ya’yan APC da wasu masu rike da mukamai suna ta ficewa a cikin jam’iyyar ba ka ganin shugaban kasa Buhari zai iya samun tangardar kuri’u?
Yanzu kamar nan Bauchi, banda jihar da aka haifi Buhari ina jin baida inda yake takama da ita kamar Bauchi, a wani gefen ma za mu iya cewa ko jiharsa ta haihuwa babu jihar da take baiwa Buhari kuri’un da suka dace, amma a yanzu muna fargabar a jihar Bauchi din ma kuri’un da Buhari zai samu a 2019 ba zai kai yawan kuri’un da yake samu a baya ba, kasancewar matsalolin da suke ta bijiro cikin jam’iyyar.

Wasu shawarori za ka bayar domin ganin an samu an daidaita wasu al’amuran da suke akwai a cikin jam’iyyar?
Shawara dukkanin wanda aka cuceshi, kasan hidimar siyasa ra’ayi ne, wanda duk aka cuceshi ka san babu wani abin da za ka fada masa ka ce ya dawo, zai yi wuya. In kuma ka tilasta masa ya dawo din zai iya yin zagon kasa wa jam’iyya wanda hakan ya fi muni ga jam’iyya ba fiye da mutum ya fitan kawai.

Sama da shekaru uku gwamnatin APC na mulki a jihar Bauchi, me za ka ce kan sha’anin mulkin jam’iyyar?
Sama da shekaru uku muna mulki a jihar Bauchi amma gaskiya babu wani abin da za mu zo mu gwada wa jama’a na a zo a gani, wannan maganar da na ke fadi maka gaskiya ne, APC ba ta tabuka abin a zo a gani a jihar Bauchi ba. mutane, kamar ni yanda na ke babu wasu aiyukan da za a ce gasu nan gwamnatin jihar Bauchi ne ta aiwatar a wannan lokacin, yawancin aiyukan da kake gani na hadaka ne kamar su makarantun Firamare, Sakandari, kamar su ginin kananun asibiti da irin wuraren shan magani dukka, da wuraren samar da ruwa dukkaninsu za ka samu aiyuka ne na hadaka ba wai gwamnatin jihace ta ke yinsu ba. irin aiyukan, gwamnatin tarayya tana ciki, gwamnatin jiha tana ciki, kananan hukumomi dukka suna ciki, hadi da kungiyoyin bayar da tallafi na kasashen waje duk suna ciki, a irin wadannan aiyukan ka ga ba gwamnatinmu bace ta aiwatar. Amma ka dauki wani zunzurutun aiki ka ce gani nan sai ka sha wuyar nunawa. Sai dai ka bincika ka ji an bayar da kwangiloli, kana tabawa sai a ce maka an bayar da aikin hanya, ina hanyoyin da aka yin? Aikin hanyar da ya dace a yi a shekara daya an shafe shekaru uku da rabi ko daya bisa ukun aikin ba a kammala ba, ka ga ai akwai matsalar rashin tabuka aiyukan a zo a gani.

Idan jama’an jihar Bauchi basu gamsu da mulkin APC ba; wacce jam’iyya kake ganin za su yi a 2019?
Ai yanzu maganar jam’iyya ma babu shi a zaben nan da za mu yin a 2019. Kuma jama’a za su gani, mutum za a yi ba jam’iyya ba, duk jam’iyyar da nagartacccen mutum ya fito a ciki lallai ita jama’a za su yi, kuma itace ta dace da yanayin da jihar Bauchi take ciki a yau. Za a zabi mutumin da tsarinsa ya dace da jihar da kuma manufar mutum, duk abin da mutum ya shuka shi zai girba sunan wannan zaben da za a yi a 2019 kenan, amma ba wai jam’iyya kaza ba.

Idan aka yi maganar aiyuka da ci gaban jihar Bauchi, ba gwamnan jihar kadai ya dace a harara ba, kasancewar shugaban kasa ya baiwa wasu ‘yan jihar Bauchi mukamai a tarayya manya-manya ana ganin basu iya kawo wa jihar wani abin ci gaba ba, su me za ka ce a kansu?
Lallai rashin tabuka aiyukan da za su ciyar da jihar Bauchi da wadannan masu manyan mukaman suka yi lallai abin kaico da tir ne. amma wasu sai ka ji suna ce maka wai su fa an basu kujerar nan amma dai su ba ‘yan siyasa bane, sai kuma su mance wanda da ba din siyasar ba; ba za su zo wannan wajen da suke a kai ba. wasu din kuma da suke ikirarin suna yi sai ka tarar suna yi ne kawai wa ‘yan gidansu, ‘yan garinsu wannan bai dace ba, domin ya dace ne a ce sun sani jihar Bauchi ne ya dace su kawo mata ci gaba ba wai daidaikun ‘yan uwansu ba. zancen gaskiya ya kamata su fito su yi aiyukan da za su taimaka wa shugaban kasa, domin mukaman da suka samu lallai da sune ake iya taimaka wa gwamnatin tarayya, amma sai gashi sun ki yin aikin, abin takaici ma ko shiga cikin jama’a basu yi, basu yarda jama’a su je kusa da su, ta yaya ne za su taimaki shugaban kasa a jikin talakawa da irin wannan ababen da suke yi?, muddin Buhari zai yi iya kokarinsa wajen baiwa ‘yan jihar Bauchi mukamai masu muhimmanci a tarayya amma su wadanda aka basu mukaman su gaza taimaka wa jama’an jihar Bauchi ai gara muce da su gara babu su, ya dace su yi amfani da dan wa’adin da ya rage su taimaka wa jama’an jihar Bauchi domin a don haka ne ma Buharin ya basu kujerun.

Me za ka ce da talakawa a wannan lokacin?
Kamar yadda shugaban kasa ya shaida cewar a zabi cancanta, lallai nima ina kiran jama’a kowa ya shirya zaban cancanta. Domin babu yadda za a yi muna ji muna gani mutum ya gaza yin komai amma kuma a sake zabansa. Balle wadandan muka ga kamun ludayinsa, don haka jama’a su zabi cancanta su kauce wa maganar wai sai jam’iyya kaza.

cin da ta tafka wa mambobinta. KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi ga hirar:

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!