Saraki Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tony Anenih — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Saraki Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tony Anenih

Published

on


Da sanyin safiyar yau Laraba 6 ga watan Nuwamba 2018 ne, shugaban Majalisar Dattijai Dakta Abubakar Bukola Saraki ya jagoranci tawagar ‘yan Majalisar Dattijai zuwa gidar marigayyi  tsohon Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Cif Tony Anenih don yi wa iyalansa ta’aziyya a bisa rasuwarsa.

Tawagar shugaban Majalisar Dattijan Dakta Bukola Saraki ya hada da mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ike Ekweremadu da sauran wasu ‘yan majalisar da dama, in da suka samu tarba daga iyalan marigayyin karkashin jagorancin babban dan marigayyin Mista Tony Jr.

A cikin jawabinsa ga iyalan marigayyin Cif Tony Anenih, shugaban Majalisar Dattijai Dakta Bukola Saraki ya yi tsokaci a kan irin gaggarumin gudummawar da marigayyin ya bayar wajen bunkasar jam’iyyar PDP, tare da kuma ganin an samu hadin ka kasa, ya kuma yi addua Allah ya gafarta masa.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!