Gidauniyar MTN Ta Bayar Da Tallafin Karatu Na Naira Biliyan 1.27 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Gidauniyar MTN Ta Bayar Da Tallafin Karatu Na Naira Biliyan 1.27

Published

on


Gidauniyar Kamfanin sadarwa ta MTN ta sanar da cewar, ta kashe Naira Biliyan 1.27 wajen samar da gurbin karo karatu ga wasu daliban da ke kasar nan.
A cikin sanarwar da gidauniyar ta fitar a ranar lahadin data wuce ta bayyabna cewar a cikin shekaru goma da suka wuce tana gudanar da shirin sama da dalibai 6,500 suka amfana da samun goraben karo karatu a fannin kere-ker, fasaha lissafi da kuma sauran darussa a jami’oin dake kasar nan da Kwalejin karau dake kasar nan.
Acewar Gidauniyar ta kuma samar da irin yawan wadannan dailban da a kalla suka kai kashi 70 bisa dari a jami’oin dake kasar nan.
Gidauniyar ta kara da cewa, a cikin shekarar 2009, ta shiga sahun manyan kamfanoni na duniya dake bayar da guraben karo karatu a cikin shirin dalibai na STEM.
Gidauniyar ta kara da cewa, wasu daliban sune suka samo guraben karo karantun, inda ita kuma gidauniyar ta biya masu kudin karatun.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kafin dalibi ya amfana da gurbin karo karatun na MTN, sai anyi masa jarrabawar gwaji kuma sai wanda ya samu sakamako mai kyau ne zai amfana da shirin.
Ana kuma bukara daliban su samu maki day a kai yawan a kalla 3.5 ,inda za’a biya masa Naira 200, 000

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!