Ibekwe: Mace Mafi Girman Mukami A Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Ibekwe: Mace Mafi Girman Mukami A Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya

Published

on


A makon da ya gabata ne Babban Sifeton ‘Yan sandan kasar nan, Ibrahim Idris, ya adamta wata Jami’ar ‘yan sanda mai suna, Patience Ibekwe Abdallah, da sabuwar lambar mukamin da rundunar ta ba ta, ta Mataimakiyar Shugaban ‘yan sanda na kasa, (DIG). Hukumar ‘yan sanda ne ta amince da yi wa wasu jami’an ‘yan sanda uku karin girma daga mukamin (AIG), zuwa mukamin Manyan Mataimakan Babban Sifeton na ‘Yan sanda, (DIG). A cikin su ne akwai, Patience Ibekwe Abdallah, wacce take mace tilo a cikin su, inda take gab da kafa tarihin kasancewa mace ta farko mai mukamin babban Sifeton ‘yan sanda ta kasa.
Kafin ta samu mukamin AIG, an taba nada ta Kwamishiniyar ‘yan sanda a Jihar Ebonyi, a shekarar 2015. A lokacin aikin nata ne a Jihar ta kaddamar da rundunonin nan biyu na musamman da suka shahara wajen magance ayyukan ‘yan ta’adda da sauran miyagun ayyuka masu suna, ‘Show of Force’ da ta ‘Walk Down Crime. Rundunoni biyun da manyan masu aikata laifuka a Jihar suka rika shayin su.Ta kuma hada kai da dukkanin masu ruwa da tsaki a Jihar gami da daukan matakan da suka haifar da da mai ido wajen magance aikata laifuka a Jihar. A lokacin ta ne kuma ta yi umurni da a rusa duk wasu shingayen da jami’an tsaron suke kafawa wadanda ake zargin su da tatsan matafiya a kan hanyoyin Jihar.
“A wurina, tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne aikin da na sanya a gaba. A kullum farin ciki na shi ne na ga al’umma suna sharara barcin su hankalin su kwance ba tare da fargaban komai ba,” wannan shi ne abin da ta shaida wa manema labarai a cikin wata tattaunawa da aka yi da ita a shekarar 2016.
Abdallah, ta yi aiki tukuru wajen ganin an sami zaman lafiya a tsakankanin al’ummun da ba sa ga maciji da juna a Jihar. A bisa kokarin ta ne ma ya sanya kungiyar masu haya da Babura a Jihar suka girmama ta da lambar yabo mai suna, “NNE Oma (Uwa tagari) ta Jihar Ebonyi.”
Gwamnan Jihar, Dabid Umahi, ya yi mata lakabi da mai yin aiki a cikin nishadi.
A shekarar 2016, Abdallah ta sa an kama gagararren mai aikata laifin nan, Ndubuisi Ewerem, a bisa laifin da ake zargin sa da aikata na yi wa wata karamar yarinya ‘yar shekara bakwai fyade.
An haifi Abdallah ne a ranar 7 ga watan Afrilu, 1963, ta shiga aikin dan sanda ne shekaru 29 da suka shige. Mutumiyar garin Odoje, ta Onitsha, Jihar Anambra. Mahaifinta mai suna, Mike Ibekwe, ya yi ritaya ne a mukamin Kwamishinan ‘yan sanda. Wanda ke kula da tsohuwar Jihar Gabas ta tsakiyan kasar nan, jim kadan da kare yakin basasan kasar nan a shekarar 1970.
Tana aure ne da Mustapha Abdallah, shugaban hukumar hana shan miyagun kwayoyi, NDLEA.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!