Kudaden Shiga Na Man Fetur Ya Ragu Da Naira Biliyan 403, inji CBN — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Kudaden Shiga Na Man Fetur Ya Ragu Da Naira Biliyan 403, inji CBN

Published

on


Nijeriya ta samu Naira biliyna 207.54 daga danyen ,maid a Gas da ta fitar afarkon zangon shekarar nan, inda kuma kudadden shigar ta ya ragu zuwa kamar a yadda ta yi tsamnain samu day a kai Naira Biliyan 661.38.
A cewar rahoton da CBN ya fitar, yawan na mai ya kai kashi 61 bisa dari na harajin da aka karba day a kai Naira tiriliyn 4.40 duk a shekarar, inda kuma na mai ya kai kashi 39.
Rahotaon ya kara da cewa, Naira tiriliyan 2.69 ko kuma kashi 4.5 bisa dari na kayan cikin gida da aka sarafa, inda kuma ribar mai ta ragu zawa a kalla kasha 30.1 bisa dari, amma sai dai, yah aura sama a farkon zangon shekarar 2017 zuwa kashi 66.5.
Babban Bankin na CBN ya kara da cewa, ribar mai ta sauka sakamakon kasafin kudi da aka kiyasta saboda ba;a samu damar sarrafa mai yadda ya kamata bah aka yawan kayan da ake son fitarwa zuwa kasar waje sun sauka kasa duk a cikin shekarar.
Kasafin kudi da aka yin na benchmark ya kai ganguna Miliyan 2.3 da ake hako a kullum, inda kuma na danyen mai ya kai Miliyan 1.90 na bpd.
Bugu da kari danyen mai da aka fitar ya sauka kasa da kasafin da aka yi na benchmark zuwa Naira Biliyan 611.38 da kuma Naira Biliyan 403.84 ko kashi 66.1 bisa dari.
Rahoton ya kara da cewa, Naira Biliyan 282.72 da kuma Naira Biliyan 22.19 daga cikin ribar mai, an tattala ta don yin kasuwancin hadaka da kuma wanda dake sanya ido a kanalbarkatun mai na DPR.
Danyen mai na kasar nan, ya karu da kashi Miliyan 0.27 na bpd ko kuma kashi 16.6 a cikin farkon zangon shekarar nan daake sarrafa a kullum da ya kai yawan Miliyan 1.90 na bpd, idan aka kwatanta da wanda aka samar a shekara data wuce.
Har ila yau, tattalin arzikin kasa ya samu jimlar kudin musaya da ya kai dala Biliyan 65.84 daga watan Janiaru zauwa watan Yunin wannan shekarar.
CBN ya bayyana cewar an samu karin ne kasuwar duniya saboda yadda dala ta yi kasa.
Acewar CBN, dala Biliyan 65.84 ta karu da kashi 87.9 bisa dari idan aka kwatanta da na farkon shekrar 2017.
Rahoton ya bayyana cewar, kudin musaya ya kai yawan dala Biliyan 35.3 sabanin dala Biliyan 30.84 da kuma dala Biliyan 19.01 a zangon shera ta biyu da kuma rabin shekara 2017.
Kudin musaya da suka bi ta hanayar CBN ya kai dala Biliyan 30.54 wanda wannan kari ne da ya kai kashi 16.4 bisa dari samada na zangon shekarar farko data biyu ta shekarar 2017.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!