Ma’aikacin Gidan Mai Ya Jagorancin Barayi Wurin Yin Fashi A Gidan — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ma’aikacin Gidan Mai Ya Jagorancin Barayi Wurin Yin Fashi A Gidan

Published

on


Rundunar ‘yan sandar jihar Legas ta cafke mai kula da gidan man ‘Skepter Petrol Station’ Daniel Freedom dan shekara 20 da wani mai bayar da mai Mike Charles mai shekaru 20, bisa zargin a akwai hannuns yin fasa a wannan gidan mai da suka aiki a unguwar Igbo-Elerin da ke karamar hukumar Ojo cikin jihar Legas. Har ila yau kuma, an samu nasarar cafke sauran wadanda ake zargin suna da hannu a cikin wannan fashi wanda suka hada da Obinna Ofoma dan shekara 25, Ndukwa Junior dan shekara 22, William Okon dan shekara 22, sai kuma Tony Oluchukwu mai shekaru 28. Kwamishinan ‘yan sanda Edgal Imohimi shi ne ya bayyana wadanda ake zargi ne a gaban ‘yan jarida ranar Litinin, inda ya ce, an samu rasarar cafke wadanda ake zargi ne lokacin da rundunar ‘yan sanda suka kai mamaye maboyansu. Imohimi ya kara da cewa,“a ranar 28 ga watan Oktoba ta shekarar 2018 da misalin karfe tara na safe, muka samu bayanan sirri cewa, ‘yan fashe suna sata a gidan mai Skepter Petrol Station a Igbon-Elerin cikin karamar hukumar Ojo ta jihar Legas, inda suka yi ma masu saida mai da  kuma danda suka zo siyar man fashi.“Lokacin da muka samu bayanan, sai muka tura rundunar ‘yan sanda reshan Ilemba Hausa da kuma ‘yan sandar FSARS Na Ikeja zuwa wajen. Abun takai ci ne, kafin jami’an tsaron su isa inda lamarin ya auku, wannan ‘yan bindiga sun gudu. Duk da haka, daga baya cikin dare, mun samu nasarar cafke ‘yan bindigan a maboyansu tare da makamai wanda suka hada da bindiga guda biyu, wuka guda uku sannan sai gatari dukka mun kwato daga hannun wadannan ‘yan bindiga.    

“Lokacin da muka gudanar da bincike, sai suka bamu sunayansu kamar haka Obinna Ofoma dan shekara 25, Ndukwa Junior dan shekara 22, William Okon dan shekara 22, Tony Oluchukwu dan shekara 28, Charles Mike dan shekara 20 sai kuma Freedom Daniel mai shekaru 20. Inda dukkanin su suka bayyana cewa, mai duba wannan gidan mai wato Daniel Freedom da kuma bai bayar da mai a gidan man Mike Charles sub ne suka shirya wannan fashin a gidan mai.”

Imohimi ya ci gaba da cewa, su dai wadanda ake zargi sun amsa laifinsu na yin fashi ne a gidan mai wanda yake kusa da Igando cikin yankin Ilemba Hausa da ke jihar Legas, ya kara da cewa, suna nan suna gudanar da bincike ta yadda za su cafke sauran wannan ‘yan bindiga tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!