2019: Abin Da Ya Sa Muka Cire Sunaye 300,000 Daga Rajistar Zabe -INEC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

2019: Abin Da Ya Sa Muka Cire Sunaye 300,000 Daga Rajistar Zabe -INEC

Published

on


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta yi bayyana yadda ta cire sunayen mutum 300,000 daga rijistar masu zabe. Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, hukumar INEC ta cire sunayen mutum 300,000 daga rigistar masu zabe. Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, sun cire wadannan sunaye ne bayan da suka yi amfani da na’urar mai gane hotan zanan yatsa ‘AFIS’ inda suka gago cewa an sake daukar rigistar masu zabe fiye da guda daya. Shugaban ya yi wannan bayani ne lokacin yakwe tarbar wakilan kungiyar ECOWAS masu sa ido a kan harkar zabe wanda shugaban zaben kasar Sierra Leone yake jagoranta Mohamed Conteh a shekaran jiya. Yakubu ya kara da cewa, za su ci gaba da tsaftace rigistar masu zaben. Ya ci gaba da cewa, a ranar 6 ga watan Nuwamba har zuwa 12 ga watan Nuwamba za su ci gaba da tan-tance rigistar masu zaben a duk fadin kasar nan. Yakubu kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan dama wajen taimaka wa hukumarsa a kan bayyan duk wanda ya yi rigistar sama da daya domin a tsaftace wannan rigistar na masu kada kuri’a.“Ya ci gaba da cewa rigistar masu zaben a tsaftace yake a hannunmu, inda muka yi amfani da na’urar AFIS a makon jiya kafin in yi tafiya, amma da ya dawo sai aka sanar dani cewa an saka sunaye guda 300,000 bayan da muka yi amfani da wannan na’ura.”
“Amma wannan masu tsaftace wannan rigistan masu zabe ba suna yi bane domin hukumarmu, suna yi ne domin ‘yan Nijeriya gaba daya.“Haka dukka haka ta ce, mu zi ca baga da tan-tance masu rijistar zabe na tsawon kwanaki shida inda yadda ya kamata tun daga ranar 6 ga watan Nuwamba har zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba. A zuwa yanzu dai mun tan-tance mazabu guda 120,000 da ke das u a fadin kasar nan wannan kasa gaki daya.”
“Ina so in yi amfani da wannan dama waje sanar ‘yan kasa cewa, su yi kokari wajen duba suna yansa idan an gama tan-tance rigistar, saboda su jawo hankalin hukumamar wajen kara tsaftace rigistar masu zabn.”
Yakubu ya bayyana manufar hukumar INEC wajen gudanar da babban zaben ta shekarar 2019, inda ya tabbatar da cewa, sun gama duk wata tsarin da ya raege abin daya rage shi ne, kawai su aiwatar da wannan tsare-tsare wajen zabe.“Mun yi kyakkyawan tsari a zaben shekara 2019 wanda ba a taba yin irin ta ba kai wannan tsari ba a cikin kasar nan.”“Mun gana shirya duk wani tsare-tsare, mun gama duk wata daukar matakin da ya kamata mu dauka wajen zabe, mun gama duk aikin wani aiki na gudanar da zabe sannan kuma mun shirya tsaf wajen yin wannan zabe. Muna da dan wata matsalar game da lokacin da za mu gudunar da zaben da kuma jaddawalin aikin gudanar da wandan babban zabe ta shekara 2019. Yakubu kuma kara bayyana cewa, a ranar 9 ga watan Nuwamba da kuma ranar 10 ga watan Nuwamba hukumarsa za ta fitar da sunayen wadanda suka lashe zaben fidda gwani na kujeran gwamna na jihoji guda 29 da kuma na ‘yan majalisar dokokin jihar a duk jijojin da suke cikin karar nan baki daya.
A bangare daya kuma, shugaban Conteh ya bayyana cewa, sun zo Nijeriya ne domin su tattara da bayani a kan yadda hukumar INEC ta shirya sannn kunma take kokarinta na gudanar da wannan babban zabe mai zuwa.“Wannan shi ya kawo wannan kungiya cikin Nijeriya a kan zaben mai zuwa.“Mun sani cewa kafin mu a gudanar da zabubbukarmu, kungiyoyi kamar ECOWAS sukan bayar da umurnin da mu zo mu samu bayanan yadda ake shirya wa zaben.“Abin da ya fi muhimmanci cewa, a matsayinmu na masu saka ido a kan zabe, yana da muhimmanci mu zo mu tattauna bayanai wajen shirye-shirye gudanar da babban zaben,” inji shi.
Conteh gode wa kungiyar ECOWAS da gungiyar ECONEC da kuma sauran hokumomi ta Nijerita wadanda suka taimaka wajen gudanar da zabe a kasar Serial Leone wanda ya gudana a watanr Aprailu.
Wani daga cikin mambobin wakilan tsowon jaroran kun gutar wajen gudanar da zabe a kasar Chana Mista Remi Ajibewa ya bayyana cewa, hukumar za ta yi amfani da wannan shiryeshirye wajen gana wa duk wadansu suke kungiyoyi masu saka idano a kan zaben a cikin wannan kasa baki dayansa. A ciwar kungiyar yadda jami’an tsaro da ungiyoyi masu zaman kansu da kuma dukkan jam’iyyun siyasa domin gudanar da zace mai inganci a babbab zabe ta shekarar 2019.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!