An Gargadi Masu Hidimtawa Kasa Da Su Guji Shiga Siyasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

An Gargadi Masu Hidimtawa Kasa Da Su Guji Shiga Siyasa

Published

on


Darekta Janar na hukumar NYSC ta masu hidimtawa kasa, Birgediya Janar Sule Kazaure, ya hore masu hidimtawa kasa da su guji cusa kansu cikin harkokin siyasa, musamman hulda da wakilan jam’iyyun siyasa da kuma ‘yan takara a zabukkan shekarar 2019 da muke fuskanta.

Janar din ya yi wannan kiran ne a yayin da ya halarci bikin rantsar da masu hidimtawa kasar a jihohin Abiya da Jigawa, inda ya yi jawabin jan hankalin a sansanin horar da masu hidimtawa kasar.

‘In ku fita daga sansanin nan, ku tabbata kun yi mu’amala da ta dace da al’ummar da aka turo ku wajensu don ku hidimta ma kasa, ku ‘yan hidimar kasa ne ba ‘yan siyasa ba, don haka ba ruwanku da siyasa, kada ku kuskure ku shiga wata jam’iyyar siyasa, in an dauke ku aikin malaman zabe, to iyakar abinda za ku yi shine gudanar da zabe.’ Inji Janar kazaure

Darektan ya umarci masu hidimar da su tabbata sun taimakawa al’ummar da suke samu kansu a cikin ta, sannansu tabbata sun kiyaye dokokin hukumar da ta tura su hidimar kasa, inda aka jadadda musu cewa ba aikin addini ko na siyasa aka tura su suyi ba, an tura su suyi wa kasa da al’ummar kasa aiki ne.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!