Ba Zan Koma Manchester United Ko AC Milan Ba – IBRAHIMOVIC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ba Zan Koma Manchester United Ko AC Milan Ba – IBRAHIMOVIC

Published

on


Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da PSG da Juventus, Zlatan Ibrahimobic ya bayyana cewa bashi da burin sake komawa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United ko AC Millan kamar yadda rahotanni suke fada.
Dan wasan mai shekara 37 a duniya tauraruwarsa dai tana haskawa a kasar Amurka a kungiyar kwallon kafa ta LA Galady halin dayasa aka fara rade radin cewa ko zai sake komawa nahiyar turai ya ci gaba da buga wasa.
Sai dai tuni dan wasan ya karyata rahoton inda yace yanajin dadin zaman kasar Amurka kuma babu maganar komawa daya daga cikin tsofaffin kungiyoyinsa daya bugawa wasa a baya wato Manchester United ko AC Millan.
“Tabbas akwai kungiyoyin da suka nuna cewa in koma turai inci gaba da buga wasa saboda sunga yadda nake kokari amma Magana ta gaskiya bani da wannan tunanin saboda inajin dadin zamana a kasar Amurka” in ji dan wasan wanda ya taba bugawa kungiyar Ajad wasa yana matashi
Ya ci gaba da cewa “Banzo kasar Amurka domin hutawa ba kamar yadda ragowar ‘yan wasa sukeyi saboda nazo ne domin in samu nasara a wasanni sannan in kafa tarihi kuma itama kungiyar tanada irin wannan burin saboda haka babu inda zani”
Kwantaragin dan wasan dai zai kare ne a shekara ta 2019 hakan yasa aka fara tunanin ko ganin yana kokari zaisa ya canja shawara domin yadawo nahiyar turai da buga wasanninsa amma kuma dan wasan yace ba haka ba.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!