Bikin CIIE Ya Shaida Kyakkyawar Makoma A Fannin Kimiyya Da Fasaha — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Bikin CIIE Ya Shaida Kyakkyawar Makoma A Fannin Kimiyya Da Fasaha

Published

on


An fitar da mota ta farko dake iya yin tafiya a sama mai suna

Aeromobil, wadda take da fasahohin musamman 40 a gun bikin CIIE, taken

aikin fitar da motar shi ne “Makoma tana nan”, wannan aiki ya zama

aiki na musamman a gun bikin CIIE a wannan karo.

A gun bikin, an gabatar da sabbin fasahohi, da kayayyaki fiye da 100 a

duniya, wadanda suka shaida tunanin yin kirkire-kirkire na dan Adam.

Hukumomin yin nazari da kamfanonin samar da kayayyaki na kasa da kasa

sun fitar da sabbin fasahohi, da kayayyaki karo na farko a gun bikin

CIIE, a wani mataki na kara maida hankali sosai ga kasuwar kasar Sin,

da kuma kokarin da Sin ta yi wajen tabbatar da ikon mallakar ilmi a

shekaru da dama da suka gabata.

A halin yanzu, kasar Sin ta shiga matsayi 20 na gaba, a jerin sunayen

kasashe da suka fi yin kirkire-kirkire a duniya, wanda hukumar kula da

ikon mallaka ta duniya ta gabatar. Aikin yin kirkire-kirkire ya sa

kaimi ga kasar Sin, wajen samun ci gaba mai inganci. Kana kasar Sin ta

shiga dukkan yarjejeniyoyin tabbatar da ikon mallakar ilmi na duniya,

yayin da yawan tambarin cinikin da aka nema, da yiwa rajista ya kai

matsayin koli a duniya a shekaru 16 a jere, kana yawan rokon mallakar

fasahohi ya kai matsayin koli a duniya a shekaru 7 a jere.

A matsayin muhimmin dandalin tattaunawa na ikon mallakar ilmi da aka

gudanar a gun bikin na CIIE, taron tabbatar da ikon mallakar ilimi, da

yin kirkire-kirkire na duniya da aka gudanar a ranar 6 ga wannan wata,

ya ja hankalin jami’ai, da masana, da wakilai daga kasashe da yankuna,

da hukumomin duniya fiye da 20, wadanda suka tatttauna kan batun

tabbatar da ikon mallakar ilmi, da samun ci gaba ta hanyar yin

kirkire-kirkire, da samar da yanayin ciniki na duniya mai inganci.

Wannan ya shaida cewa, kasar Sin ta dauki alhakinta wajen tabbatar da

ikon mallakar ilmi na duniya.

(Mai Fassarawa: Zainab Zhang, ma’aikaciyar sashen Hausa ta CRI)

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!