Dalilin Da Ya Sa Atiku Ke Karbuwa A Kano –Bagobiri — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Dalilin Da Ya Sa Atiku Ke Karbuwa A Kano –Bagobiri

Published

on


An bayyana yanayin da Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya sami nasara a zabe na fidda gwani na zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben da aka yi a Fatakwal wata manuniya ce ta nasara da ta nuna dukkan shiyyoyin kasar nan sun karbi takarar Atiku hannu biyu da ha kan alamace da zai samu gagarumar rinjaye a zabe mai zuwa na kasar nan. Daraktan yakin neman zaben shugabancin kasa na Atiku Abubakar reshen jihar Kano Alhaji Yahaya Umar Bagobiri ya bayyana haka da yake zantawa da wakilimmu.
Ya ceyana ganin wannan nasara ta takarar Wazirin Adamawan ta samu ne sakamakon an tanyance anga shi ne kadai zai iya fidda kitse daga wuta,wanda ta silarsa za’a kaiga nasara a kauda Gwamnatin APC daga mulkin kasar nan duba da halinda ake ciki tun daga 2015 data karbi mulki cikin kwanciyar hankali al’umma suna kasuwanci,suci abinci sau uku suna iya zirga-zirga hankali kwance,amma yanzu talaka na cikin kaka-na-kayi,babu aiki ga hauhawar farashin kaya.
Alhaji Yahaya Bagobiri ya bada misali da cewa yanzu in kana da iyali da ya’ya biyar in samun da kake bai wuce Naira 1,500 ba, ba za a iya cin abinci a wuni ba bare ya’yan naka suje makaranta ko a dinka musu kaya ko a biya musu kudin makaranta balle in kana da abin hawa ace kana zuba masa ma i yau da kullum kana zirga-zirga hatta mai zai yi tashin gwauron zabi da PDP ta barshi a N85.Yanzu an mai da shi Naira 145. matsaloli daban-daban farashin kayan abinci ya nunka nunki, haka kudin aikin Hajji abubuwa a fili suke karara matsaloli sun addabi al’ummar Nijeriya,in kana lissafa matsaloli da APC ta jefa kasa sai kaji mutane Allah-Allah suke lokaci yayi su kauda Mulkinta ta ishesu. Zabe ne yanzu ake so ayi tsa kanin koshi da yunwa, da kuma aikinyi da zaman banza da kuma sauki da hauhawar farashi.
Bagobiri ya bayyana tasirin da Buhari yake da shi a baya a jihar Kano ta kyautata tsammani n za a sami wata nasara in yah au mulki ne, sai aka ga kusan shekaru hudu ba sauki sai wahala da aka shiga. Sanna shugaba Buhari ba masoyin al’ummar Kano bane, makiyin sune bisa dalililai da in aka duba manyan mutane a jihar Kano da aka yi rashinsu bai taba zuwa gaisuwa ba, iftila’i daya samu a Kano na gobara a kasuwanni wanda mutane suka rasa Biliyoyin Naira bai taba zuwa ya jajanta ba. Kuma aiki da ake magana a Kano, ba aiki kwaya daya wanda ya yi a Kano. Wannan ya nuna ba masoyin Kano bane. Duk dan Kano daya isa jefa kuri’a yasan abin da yake ba zai sake yarda ya jefawa Buhari kuri’a ba.
Ya kara da cewa, halin da PDP ta tafi tabar kasar nan na talaka na iya cin abinci sau uku ya dika sutura, yana iya hawa mashin ko mota ya zuba maid a sauki, kasuwanci na garawa ana samun riba, yanzu ba wadannan abubuwa su wadanda aka dora da suka ji dadin dimokradiyya yanzu sune suke jayayya suke tunanin har yanzu jama’a suna goyon bayansu, amma za su gane kuskurensu sai lokacin zabe ya zo za su gane kurensu.
Ya ce, ‘yan APC in suna maganar tsaro ya samu a ina ne? Kwanannan a nan Kano anje garin Madobi an kama daraktan mulki ma’aikata aka yi harbe-harbe aka sace shi, wanda a baya babu irin wannan masifar lokacin PDP yanzu in zaka yi tafiya rayuwarka tana cikin hatsari, hasali ma duk yankin Arewa ba inda ake zaune lafiya sabanin ada Boko Haram maganace ta Miduguri, Yobe da Adamawa, amma yanzu jihohi 19 ba inda zaka je kaga ana kwance lafiya.Yanzu daga nan zuwa Zamfara wane hali suke ciki, wasu kananan hukumomi an tarwatsa su, abin da ya yi Zamfara shi ya yi Sakkwato ya yi Kebbi, wadannan jihohi suna karkashin matsala ta rashin tsaro hakama Katsina barayin shanu suna zuwa gida su kama shanu mutane su kashe mutane. Haka Bauchi da Gwambe da Kogi da Filato ba inda ake zaune lafiya.Yanzu ka gwada tafiya wata hanya sai a kamaka ace sai an bada kudin fansa, ina zaman lafiya yake ban da karya da ake kullum ace an samar amma al’umma sun san ba haka bane.
Alhaji Yahaya Bagobiri ya ce, musu cewa Atiku bai wa kasa komai ba a baya daya sami dama ta mataimakin shugaban kasa,wasu ne kawai da suke kinsa suke fada, wanda shi makiyi inka fada ruwama sai ya ce, ka tada kura, amma an san mataimaki shugaban kasa iya kaci ya nemi alfarma wurin shugaba ya yi masa, in bai masa ba, balalai bane, sannan a wannan lokaci sun sami matsala da abokin aikinsa shugaban kasa da yake wa mataimaki a wancan lokaci kusan duk tsawon mulkin. Amma idon maganace ta gina al’umma ko tallafi aje Adamawa a tambayi me yayi musu.Ya bude kanfanoni da dama ya debi dinbin ma’aikata matasa aiki sama da 50’000. Iya abin da zai yi na arzikinsa yanayi.
Alhaji Bagobiri ya ce, Wazirin Adamawa dan takarar shugabancin kasa na PDP ba a taba kamashi da ana zarginsa ya dauki can koya taba can ba. Mutum ne ya yi aiki kuma ya gama lafiya, ba a taba zarginsa ba, ya kuma san hakkin mutane a bangaren aiki. Mutum ne dan kasuwa da yake da nasibi a cikinta, ya san darajar kasuwanci ya san kasuwa sama da shekara 30, kuma dan siyasa ne yasan siyasa da yan’siyasa da darajar siyasar wanda ya hada abu uku da yake da wahala ace bai san hakki ko darajar dan adam ba.
Alhaji Yahaya Umar Bagobiri ya ce, idon mutanen Kano suka dunkule suka ba shi goyon baya, rashin aiki zai ragu za a bunkasa kasuwanci zai maganta taka halaye da akewa yan kasuwa da sai sun sun fita sun sayo kaya an kawo kasuwa sai azo a kwashe ace na fasa kwauri ne,Waziri ba zai yarda da irin wannan ba. Mutanen Kano daga yadda abubuwa suke da yadda aka yi musu rikon sakainar kashi a wannan mulki na Buhari ba za su kara zabar APC ba.Wanda suke fata zabe mai zuwa mutane su fito su canja wannan canji da aka yi domin canjin ba shi bane na alheri su canja wannan canji su zabi PDP su zabi Atiku a matsayin shugaban kasa don Nijeriya ta dawo hayyacinta.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!