Kotun Kasar Masar Ta Daure ‘Yan Kungiyar ISIS Su 65 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotun Kasar Masar Ta Daure ‘Yan Kungiyar ISIS Su 65

Published

on


Babbar kotun kasar Masar ta yankewa wasu mutum 65 da ake zargin ‘yan kungiyar ISIS ne, hukuncin wa’adin gidan yari daban-daban, ana zargin mutanen su na da alaka da Abubakar Baghadadi na kasar Iraki, ‘yan ta’addan suna karkashin shugabancin wani mutum ne mai suna Amir Mustafa Ahmad Abdelaal.

Mutum 18 daga cikin ‘yan ta’addan an yanke musu hukuncin daurin rai da rai, sannan mutum 41 kuma na yanke musu hukunci shekaru 15 a gidan kaso, sai yara kanana guda shida da aka yanke wa hukuncin zaman gidan gyara halinka na shekaru biyar, sannan an wanke wasu mutum biyu da ba same su da wani laifi ba.

Tun bayan da sojojin kasar suka hambare zababben shugaban kasar Masar din, Muhammad Mursi a cikin shekarar 2014, ake samun tada kayar baya daga kungiyoyi daban-daban na ‘yan tada kayar baya a kasar Masar din, jami’an tsaron kasar sun hallaka sama da ‘yan ta’adda 450 a cikin shekarar nan.

A makon da ya wuce ‘yan ISIS din sun dauki nauyin wani hari da aka kaiwa Kiristoci Kibdawa, a gundumar Minya dake kudancin kasar masar din, inda harin ya yi sanadiyyar mutuwar Kibdawa 7.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!