Matasa Masu Zaman Banza Ba Karamar Barazana Bace Ga Tsaron Kasa –Gwamnatin Tarayya   — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Matasa Masu Zaman Banza Ba Karamar Barazana Bace Ga Tsaron Kasa –Gwamnatin Tarayya  

Published

on


Gwamnatin tarayya ta ce hauhawar yawan adadin matasa masu zaman banza ba karamara barazana bace ga tsaron kasa, ba kawai ga tsaron kasa ba, harda cigaban tattalin arziki ma.

Gwamnatin tarayya ta na neman hadin gwiwar kungiyar kwadago ta duniya domin ganin ta yi wa wannan annobar birki, gwamnatin za ta samar da ayyukan yi ga matasan don rage wannan barazanar, domin matasan kasar nan su na da hazakar yin sana’a.

Duk kasar da ya zama akwai matasan da basu da aikin yi, to kasar za ta shiga mugun matsalar tsaro da tashin hankali, sannan za a samu tsaiko a ci gaban tattalin arzikin kasar, don haka dole a dakile wannan matsalar kafin ta kai matakin da za ta fi karfin gwamnati.

Ministan kwadago na Nijeriya, Mista Chris Ngige ya ce gwamnatin su a shirye take wajen ganin ta shawo kan wannan matsalar da take nema ta addabi kasar nan, kuma ya tabbatar da cewa gwamnati za ta cimma nasarar dakile matsalar cikin kankanin lokaci.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!