Ribar Kamfanin Flawa Ya Fadi Ga Kashi 85.71 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Ribar Kamfanin Flawa Ya Fadi Ga Kashi 85.71

Published

on


Rahoto ya sanar da cewar, ribar kamfanin Flour Mills of Nigeria Plc ta fadi da kashi 85.71.
bayanin hakan yana kunshe ne a cikin sanarwa ta watanni shida zuwa watan Satumbar 2018 da aka baiwa NSE, inda hakan ya nuna cewar, bayan biyan bashi da kmafanin ya yi, data kai ta Naira biliyan 5.04 ribar kamfanin ya sauka daga Naira biliyan, 9.35 a cikin shekarar 2017. Kamafin ya fitar da sanarwar ce a ranar juma’ar data wuce, inda rahoton ya kara da cewar ribar ta sauka ne saboda kalubalen aikin da ake gudanarwa a yankin Apapa dake cikin jihar Legas. Manajin Darakta na rukunonin kamfannin Mista Paul Gbededo ya ce, aikin na Apapa ya janyowa kamfanin babban kalubale wajen aiwatar da ayyukn sa, inda hakan ya yanyo kamfanin baya iya sarrafa kaya ma su yawa kamar yadda ya sana yi. Sai dai ya ce, kamfanin shiyar sa ta karu na kayan da yake sarrafwa. Acewar rahoton, kamfanin ya samu sukunin rabarwa da kuma sayar da kayan da ya sarrafa da suka kai na kashi 49 da kuma Naira biliyan samun ribar Naira biliyan 4.13 a cikin watanni shida zuwa watan Satumbar 2017, inda aka samu Naira biliyan 2.77 a cikin shekarar 2017. Raoton ya kara da cewar, kashi shida da aka samu na zuba jari ya karu zuwa Naira Miliyan 290, sabanin Naira Miliyan 270 da aka samu a 2017. Rahoton ya ci gaba da cewa, an samu karin ne saboda zuba jari da aka yi na gajeren zango. Har ila yau, kamfanin ya samu kashi 31 bisa dari na kudi daga ckin Naira biliyan 16.27 a cikin zangon shekarar 2017 zuwa Naira biliyan 11.23 a zangon shekara ta biyu ta 2018.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!