2019: NYSC Ta Nemi  Mambobinta Su Taimaka Kan Aiwatar Da Sahihin Zabe — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

2019: NYSC Ta Nemi  Mambobinta Su Taimaka Kan Aiwatar Da Sahihin Zabe

Published

on


Bisa karatowar babban zaben 2019 a Nijeriya, hukumar da ke kula da ‘yan yi wa kasa hidima, (NYSC), ta bukaci mambobinta da za a dauke su aikin wucin gadi wajen gudanar da aikin zabe, da cewar su taimaka wa hukumar zabe ta kasa INEC wajen tabbatar da gudanar da sahihin zabe a 2019.

Darakta Janaral na hukumar, Birgediya Janar Suleiman Kazaure shi ne ya yi wannan kiran a cikin makon nan, sa’ilin nan da yake zagayen gani da ido a sansahin ‘yan yi wa kasa hidima masu samun horo a wannan lokacin a sansaninsu da ke Wailo, Bauchi.

Kazaure, wanda ya samu wakilcin Daraktan shalkwatan hukumar ta NYSC, Habibu Kurawa, ya ce, mambobin ‘yan yi wa kasa hidima za su ci gaba da kasancewa masu gudanar da aikinsu ba tare da daukan bangare ba, inda ya shaida cewar a bana din ma za su samar da mambobin da za su yi aiki tukuru wa jama’a domin tabbatar da an yi zabe cikin nasara a Nijeriya.

Shugaban ya bayar da tabbacin hukumar na cewar ta kammala dukkanin tsare-tsaren da suka dace, kama daga ta wajen hukumomin tsaro wadanda za su tabbatar da baiwa jami’ai masu bauta wa kasa kariya gabanin da kuma lokacin gudanar da aikinsu na zabe, kana, sai kuma ya gargadi dukkanin mambobinsu da su kaurace wa amsar kudaden ‘yan siyasa domin yin magudin zabe, ya shaida cewar duk wanda suka cafke da aikata hakan ba zai taba ji da dadi ba; kana ya nemi dukkanin wanda aka samu da aikata hakan a gaggauta sanar da ofishohinsu na shiyya da ke kusa.

Da yake tasa jawabin, babban jami’in shirin a jihar, Mr Afolayan James ya gode wa shugabansu na kasa a bisa kawo ziyarar da yayi ga sansaninsu da ke Bauchi, inda yake mai shaida cewar sansanin nasu yana da wadattun kayyaki horo da kuma ba ladaftarwa a kowani lokaci.

Ya kuma shawarci masu yi wa kasa hidima a kowani lokaci da suke rungumar hidima wa jama’a a kowani lokaci domin dacewa da taimakon jama’a a fadin jihar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!