Abin Da Ya Sa Kabilar Kolufo Ta Zabi Rayuwa A Bishiya Fiye Da Doron Kasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Madubin Rayuwa

Abin Da Ya Sa Kabilar Kolufo Ta Zabi Rayuwa A Bishiya Fiye Da Doron Kasa

Published

on


A yau filin namu zai sada ku ne da mutanen Korowai wadanda ake kira da Kolufo da ke zaune a Kudancin Papua ta Kasar Indonesiya da ke kusa da iyakar Papua ta kasar sabuwar Guinea, ‘New Guinea.’  Kiyasi ya  nuna mutanen a yanzu sun kai yawan dubu uku a doron kasa.

Al’ada

A al’adance mutanen suna rayuwa ne a gidaje da suke kerawa a saman bishiya (Tree House) suna rayuwa ne a kebe a dokar daji, domin kuwa daga baya bayannan ne ma suke iya sanin cewar bayansu akwai wasu halittun a doron kasa. A cewarsu yin gidajen nasu a saman bishiya shi ne zai ba su kariya daga makiyansu na kauyukan da suke makotaka da su ,da kuma sauran mutane daga wasu wurare. A cewarsu mutane suna dauke ne da aljanu, da kuma rauhanai masu cutarwa, A kowacce kabila tana dauke ne da gidaje hudu zuwa biyar wadanda ke da zama a can saman bishiya wanda tsawonsa daga kasa ya kai taku 140, dai-dai da mita 8 zuwa 12, ya yin da a wasu wuraren kuma tsawon gidajensu kan kai har tsawon mita 40,su kan yi amfani da itatuwa ko a ce sanduna masu karfi wajen tare gidajen a sama, su kan yi amfani da tsani mai tsawo shi ma wajen haura wa sama domin shiga gidajensu. Ba sa sanya tufafi domin kuwa mazansu da matansu su kan yi yawo ne babu komai a jikinsu. Akasari gini ko kera gidajen ya kan dauke su ne tsawon kwana uku zuwa biyar, yayin da kuma gidan zai iya zama na tsawon shekara hudu zuwa biyar kafin ya lalace, idan kuma itacen da suke amfani da shi wajen kera gidajensu ya kare su kan yi hijira ne su koma wani jejin daban domin ci gaba da zama.

Cin naman mutane (cannibalism)

Wani abin mamaki da ke faruwa tsakanin wadannan kabila, har kawo yanzu shi ne dabi’arsu ta cin naman mutane. Wato na farko dai idan mutum ya mutu, mutanen su kan fafe kan mamacin domin kwaso kwakkwalwar shi, bayan sun kwashe sai kuma su sarrafa shi su cinye, hikimar hakan a cewarsu ita ce, yana maganin cututtuka da dama, ciki kuwa har da cututtukan da suke kama kwakwalwa.

A wani bangaren kuma har ila yau idan mutum ya aikata wani gagarumin laifi, musamman ma mutumin da aka kama shi da laifi irin na Maita, wanda suke wa lakabi da “Khakhua” babba ko yaro, toh fa hukuncinsa shi ne kisa, wanda bayan an kashe shi kuma sai a sarrafa namansa a cinye. Akwai kuma lokutan da wasu matan su kan zabi cinye naman mazajensu a maimakon a bisne shi ta hanyar kona gawar, sannan su rika sarrafa tokar mamaci ta hanyoyi daban-daban suna ci,wasu rahotanni daga baya-bayannan dai suna nuna cewar mutanen Korowai sun daina al’adarsu ta cinye naman mai laifi, yayin da kuma suka yi imani da cewar akwai wata rayuwar bayan mutuwa. A cewarsu bayan mutum ya mutu, ya kan sake dawowa duniyar rayayyu, wannan hanya kuwa ita ce haihuwa domin sun ce idan mutum ya mutu a kan sake haifarsa ya dawo duniya a matsayin jariri

Abinci

Al’ummar Korowai suna rayuwa ce a kan abincin da suka noma, da kuma dukkan abin da ya taho hanyarsu. Cikin abincinsu akwai ‘Sago’ wanda suke samunsa su sarrafa shi daga bishiyar Sago, su kan kama kifi daga kogi, sannan kuma suna farautar al’adu irin ta daji, Alade irin na gida ya kasance dabba mai matukar muhimmanci a wajen wadannan mutane, domin kuwa ba’a ma cinsa sai lokacin wani kwakkwaran biki, su kan yi amfani da karnuka wajen yin farauta yayin farautar Alade kuma su kan yi ta ne ta hanyar amfani da kwari da baka.

Aure

Miji ya kan auri mace fiye da daya ko biyu a lokaci daya, amma kasancewar tsadar kudin aure ya sanya su kan yi auren dai-dai iya yadda karfinsu ya kama. Akan aurar da matan Korowai daga zarar sun kai matakin girma wanda ya kasance yawaici bayan mace ta ga al’adarta ta farko, mafi akasari tsakanin shekara goma zuwa goma sha biyar. Saki ba ya daga cikin tsarin wadannan mutane, domin kuwa fada da sasanci ya kan kasance tsakanin mata da kuma mijinta kawai, hakan ya sanya yawaicin aure suka zamto cikin

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!