Conte Ya Sha Alwashin Kai Chelsea Kotu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Conte Ya Sha Alwashin Kai Chelsea Kotu

Published

on


Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Antonio Conte, ya bayyana cewa idan har kungiyar bata biyashi hakkokinsa ba daya kamata su biyashi saboda yarjejeniyarsu zai maka kungiyar a kotu domin neman hakkinsa.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dai ta kori Conte a kwanakin baya inda kuma ta maye gurbinsa da tsohon kociyan Napoli, Mauricio Sarri, wanda a yanzu shine yake jan ragamar kungiyar bayan yabar Napoli.

Lauyoyin Conte dai suna nan suna aiki tukuru domin ganin sun kammala tattara bayanai kafin su tafi kotu sai dai kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta shirya zama domin tattaunawa da Conte amma yaki amincewa.

Rahotanni sun bayyana cewa Conte dai yana bukatar Chelsea ta biyashi ragowar kudadensa da sukayi yarjejeniya na fam miliyan 8 da dugo bakwai a yarjejeniyar fam miliyan 11 da suka kulla sai dai basu biyashi ba.

Sai dai an bayyana cewa Chelsea taki biyansa kudaden nasa ne saboda halayyar Conte mara kyau daya nuna a kungiyar ta zuwa filin daukar horo a makare da kin halartar taron masu daukar nauyin kungiyar da rikicinsa da Diego Costa da kuma ajiye motarsa a inda bai kamata ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta nemi Conte domin yaje yazama kociyan kungiyar sai dai daga baya yaki amincewa saboda rikicinsa da Chelsea bazai bashi dama yaje wata kasar yayi aiki ba indai ba Ingila ba har sai kakar wasa ta kare.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!